Babu Ma’aikacin da Ke Bin Gwamnatin Yobe Bashin Ko Anini, Inji Gwamna Buni

Babu Ma’aikacin da Ke Bin Gwamnatin Yobe Bashin Ko Anini, Inji Gwamna Buni

  • Gwamnan jihar Yobe ya bayyana cewa, jiharsa na daga cikin jihohin da ma'aikata ke samun albashi a kan kari
  • A baya wani rahoto ya shaida cewa, akwai wasu jihohi da dama a kasar nan da ke fama da rashin biyan ma'aikata albashi a kan kari
  • Baya ga batun biya a kan lokaci, karancin albashi na daya daga cikin abubuwan da ma'aikata a Najeriya ke fama dashi duba da tattalin arzikin kasars

Jihar Yobe - Gwamna Mai Mala Buni na Yobe a ranar Juma’a ya ce gwamnatinsa na kokari wajen biyan albashin ma’aikata duk da karancin kudi da jihar ke da shi, Guardian ta ruwaito.

Buni, a wata sanarwa da babban daraktan yada labaran sa, Mamman Mohammed, ya fitar a Damaturu, ya ce wani bincike da wata kafar fasaha ta BudgIT ta gudanar ya tabbatar da hakan.

Kara karanta wannan

Akwai matsala: Bankin Duniya ya yi Mummunan Hasashe a kan Halin Najeriya

Gwamna Mai Mala Buni ya ce babu ma'aikacin da ke binsa bashi
Babu Ma’aikacin da Ke Bin Gwamnatin Yobe Bashin Ko Anini, Inji Gwamna Buni | Hoto: guardian.ng
Asali: UGC

A cewar gwamna Buni:

"Rahoton binciken wanda ya tsaya a Yuli 2022, ya nuna jihar Yobe a matsayin daya daga cikin jihohin da ma'aikatan gwamnati ba sa bi bashin albashi."

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Gwamnan ya bada tabbacin cewa biyan albashin ma’aikatan gwamnati a kan kari zai ci gaba da zama babban abin da gwamnatinsa ta sa a gaba, rahoton Independent.

A kalamansa:

“Duk da karancin kudi da jihar ke da shi, wannan gwamnatin ta jajirce kuma ta tsaya tsayin daka wajen biyan albashin ma’aikata, kuma za ta ci gaba da hakan."

Buni ya kara da cewa:

"Mun kuduri aniyar tabbatar da cewa ba za mu taba kasawa wajen biyan albashin ma'aikatanmu ba."

Sai dai ya bukaci ma’aikatan da ke cin albashi na jiha da na kananan hukumomi da su mayar da hankali a kan ayyukansu ta hanyar aiki tukuru, sadaukarwa da kuma jajircewa.

Kara karanta wannan

Gwamnan APC: Ba yadda za a yi Buhari ya ci bashin N1.1tr don biyan bukatun ASUU

Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) ya bayyana cewa, a baya BudgIT, a 2020 ta sanya jihar Yobe ta biyu cikin jihohi mafi kyawun sarrafa kudi a kasafin kudin kasar.

Gwamna Zulum Ya Tabbatar Wasu Malamai Na Karban Albashi Kasa da N11,000 a Wata

A wani labarin, gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Umaru Zulum, ya tabbatar da cewa akwai wasu Malamai na matakin kananan hukumomi, LEA da ke karɓan albashin N11,000 duk wata ko ƙasa da haka.

A wata sanarwa da gwamnan ya fitar a shafinsa na Twitter, Zulum ya ce baki ɗaya Malaman Sakandire da ke faɗin jihar na karɓan Albashi dai-dai da ƙunshin mafi karancin albashi N30,000.

Mai magana da yawun gwamnan, Malam Isa Gusau, ne ya yi wannan bayanin yayin da yake martani kan wasu Hotunan da ke yawo a kafafen sada zumunta, waɗan da ke nuna sakon Albashin wasu Malamai ƙasa da N10,000.

Kara karanta wannan

Yajin Aikin ASUU: Ba Dole Ne Sai Kowa Ya Yi Digiri Ba, In Ji Gwamnan APC

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.