An Ba Dan Sanda Kujerar Hajji Da N250,000 Saboda Mayar Da Dalolin Tsintuwa

An Ba Dan Sanda Kujerar Hajji Da N250,000 Saboda Mayar Da Dalolin Tsintuwa

  • Wata jarida ta yanar gizo mai suna Katsina City News ta yiwa wani dansanda kyautar Naira 250,000 mayar da Dala 800 da ya tsinta ga mai shi
  • Nura Mande da ya dawo dala 800 kudin guzurin tafiyar aikin hajji da wata hajia daga jihar Katsina ta batar a sansanin alhazai
  • Hon, Ali Abu Albaba, a lokacin da yake gabatar da kyautar kudi ga Nura Mande ya ce ba kowa bane zai tsinci makudan kudi ya maida wa mai shi su ba

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Jihar Katsina - A ranar Alhamis ne wata jarida ta yanar gizo mai suna Katsina City News ta yiwa wani dansanda kyautar Naira 250,000 da kujerar aikin Hajji saboda ya mayar da Dala 800 da ya tsinta da wata maniyyaciya ta batar. Rahoton Daily Nigeria

Kara karanta wannan

Harin Cocin Owo : MURIC ta Bukaci Gwamnan Ondo ya Biya Fulani Diyya Tunda Gaskiya Ta Fito

Dan sanda Najeriya mai suna Nura Mande da ya dawo dala 800 kudin guzurin tafiya da wata hajia ta batar a sansanin alhazai na Jihar Katsina gabanin tafiyar ta aikin hajjin bana da ya gabata.

Dan Majalisar Dokokin daga jihar Katsina, Honorable Ali Abu Albaba ne ya jagoranci gabatar da kyautar ga Nura Mande a madadin mawallafin jaridar Katsina City News a Hedikwatar yan Sandan jihar.

Police
An Ba Dan Sanda Kujerar Hajji Da N250,000 Saboda Mayar Da Dalolin Tsintuwa FOTO Guardian.ng
Asali: UGC

Honorable Abu-Albaba ya ce jaridar ta dauki nauyin yiwa Abun Mande kyautar ne saboda gaskiya da tausayi da ya nuna.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Abu Albaba ya kara da cewa ba kowa ne zai tsinci makudan kudi da babu wanda ya gan shi ya mayar wa da mai shi su ba kamar yadda Aminiya ta rawaito

Dan Majalissar ya ce bayan tukwicin da dan sandan ya samu, daga gidan jarida an kara samu wanda ya shi kyautar kujerar Hajji don sauke farali a shekara mai zuwa.

Kara karanta wannan

Yarda Zai Yi Wa Tinubu Aiki ya Jefa Gwamna a Matsala, Ana yi wa Addininsa Barazana

Mun Kashe Triliyan N3.2 Da Muka Kwato Daga Barayin Gwamnati —Malami

A wani labari kuma, Babban Lauyan gwamnati kuma Ministan Shari’a, Abubakar Malami, yace Najeriya ta kwato Naira triliyan 3.2 da aka sace daga kasar aka boye a bankuna daban-daban a duniya.Rahoton Aminiya

Abubakar Malami ya bayyana haka ne a lokacin da ya gana da yan jarida a Fadar shugaban kasa a ranar Alhamis

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Tofa avatar

Ibrahim Tofa

Online view pixel