Abin da Buhari ya Shaidawa ‘Yanuwan Fasinjojin Jirgin da Aka Dauke Ya Bayyana
- An samu labarin abin da Shugaban kasa ya fadawa iyalan fasinjojin jirgin kasan da ke tsare a jeji
- Muhammadu Buhari yace ana ta bakin kokari domin ganin ragowar mutane 31 sun dawo gida
- A jawabin da Femi Adesina ya fitar, yace gudun a kashe wasu ya hana sojoji suyi luguden wuta
Abuja - Shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana cewa kusan mutane 31 da aka dauke a jirgin kasan Abuja zuwa Kaduna suna tsare har yanzu.
Daily Trust ta rahoto cewa Mai girma shugaban kasa ya bayyana haka ne a sa’ilin da ya hadu da ‘yanuwan wadannan Bayin Allah a fadar Aso Rock.
Mai magana da yawun shugaban Najeriya, Femi Adesina yace Muhammadu Buhari ya fadawa wakilan mutanen irin kokarin da gwamnati take yi.
Adesina yace Mai girma Buhari ya nuna cewa an yi kokarin ganin an kawowa iyalan wadanda abin ya shafa sa’ida, a kuma magance aukuwar haka.
Rahoton yake cewa Shugaban Najeriyan ya yi masu bayanin cewa abin da ya hana ayi amfani da karfin soja wajen kubutar da sauran wadanda ke tsare.
Hadimin shugaban kasar yace gwamnati na bakin kokari domin a ceto ragowar mutanen cikin koshin lafiya, don haka aka fasa yin luguden wuta.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Jawabin Muhammadu Buhari
“An sanar da ni cewa a kidayar karshe kusan mutane 31 suka rage a hannun masu garkuwa da mutane, kuma kokarinmu shi ne mu dawo da su ga iyalansu.
Za a iya fahimtar hankula za su tashi, an ba mu shawarar amfani da kayan yaki domin kubutar da wadanda ke tsare. An yi tunani, an yi la’akari da hakan.
Amma babu tabbacin za a iya cin nasara wajen ceto kowa ba tare da an yi barna ba, hakan ta sa aka yi watsi da wannan shawara, ba saboda ana so ba.”
Yadda Dan Najeriya Ya Badda Kamanni A Matsayin Mace A Facebook, Ya Damfari Dan Indiya Naira Miliyan 31
“Babban burinmu shi ne mu kubutar da kowane lafiya lau ba tare da ciwo ba.”
- Muhammadu Buhari
An fara samun sauyi yanzu
A karshen jawabinsa, Buhari yace an fara samun nasarori game da batun rashin tsaro bayan umarnin da ya bada na ganin cewa sun kawo zaman lafiya.
Sabiu Muhammad ya yi jawabi a madadin wakilan mutanen nan da sun shafe watanni a hannun ‘yan ta’adda, yace sun kagara sus a ido a kan masoyansu.
Bashin Paris Club
A baya an samu rahoto cewa Shugaba Muhammadu Buhari ya hana a fara cire bashin da ake bin Gwamnonin Jihohi daga tsohuwar yarjejeniyar Paris Club.
Ministar kudi da AGF sun roki a soma karbe bashin daga FAAC, amma majalisar FEC ta rinjaya a kan ra’ayin Gwamnoni, ganin halin da tattalin arzikin kasa ke ciki.
Asali: Legit.ng