Hotunan Yadda Aka Yi Jana'izar Sojojin Da Yan Ta'adda Suke Kashe A Abuja

Hotunan Yadda Aka Yi Jana'izar Sojojin Da Yan Ta'adda Suke Kashe A Abuja

  • An yi jana'izar dakarun sojojin Najeriya guda biyar na Guards Brigade da wasu yan ta'adda suka halaka su yayin harin kwanton bauna a Abuja
  • Yan ta'addan sun halaka dakarun sojojin ne da yayin da suka afka wa tawagarsu a lokacin da suke dawowa daga amsa kirar neman dauki a makarantar horas da lauyoyi
  • Manyan jami'an rundunar sojojin Najeriya sun hallarci jana'izar ciki har da kwamandoji, Staff ofisa har ma da shugaban karamar hukumar Bwari, Honn John Gabaya

FCT, Abuja - A ranar Alhamis ne aka birne dakarun sojoji na Guards Brigade da yan ta'adda suka kashe a babban birnin tarayya Abuja, Daily Trust ta rahoto.

An birne jagoran sojojin Kyaftin Attah Samuel da wasu sojoji hudu wanda suka sadaukar da rayuwarsu, a makabarta ta Guards Brigade da ke Maitama, Abuja.

Kara karanta wannan

Luguden Wuta: Jirgin Sojoji Ya Sheƙe Babban Kwamandan Yan Ta'adda, Alhaji Modu, da Wasu 50

Jana'izar Sojojin Da Yan Ta'adda Suka Kashe a Abuja
Hotunan Yadda Aka Yi Jana'izar Sojojin Da Yan Ta'adda Suke Kashe A Abuja. Hoto: @daily_trust.
Asali: Twitter

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kafin rasuwarsu, dakarun sojojin suna aiki ne tare da 7 Guards Battalion, Barikin Lungi Maitama da 176 Guards Battalion, Gwagwalada, FCT Abuja.

Ga hotunan yadda aka yi jana'izarsu a kasa:

Jana'izar Sojoji
Malaman addini suna addu'o'i yayin jana'izar sojoji. @daily_trust.
Asali: Twitter

Jana'izar Sojoji
Shugabannin sojoji suna ban girma ga dakarun da suka rasu kafin a birne su. Hoto: @daily_trust.
Asali: Twitter

Jana'izar Sojoji
Hotunan Yadda Aka Yi Jana'izar Sojojin Da Yan Ta'adda Suke Kashe A Abuja. Hoto: @daily_trust.
Asali: Twitter

Jana'izar Sojoji
Hotunan Yadda Aka Yi Jana'izar Sojojin Da Yan Ta'adda Suke Kashe A Abuja. Hoto: @daily_trust.
Asali: Twitter

Jana'izar Sojoji
Ana bawa iyalan sojojin da suka rasu kayansu. Hoto: @daily_trust.
Asali: Twitter

Jana'izar Sojoji
Iyalan Sojojin Da Suka Rasu Suna Karbar Kayansu. Hoto: @daily_trust.
Asali: Twitter

Asali: Legit.ng

Online view pixel