An Sake Kama Mutum 2 Cikin Yan Ta'addan Da Suka Kai Hari Cocin Owo

An Sake Kama Mutum 2 Cikin Yan Ta'addan Da Suka Kai Hari Cocin Owo

  • Rundunar sojojin Najeriya tare da hadin gwiwar sauran jami'an tsaro sun yi nasarar kama wasu karin yan ta'adda biyu da ke da hannu a harin cocin Owo
  • A jiya Laraba, hedkwatar tsaro ta bakin babban hafsan sojin kasa, Janar Lucky Irabor ta sanar da kama wasu yan ta'addan hudu da ake zargi da kai hari a cocin
  • Bayan kama hudun na farko, sojoji tare da DSS sun kuma sake yin nasarar kama wani Al-Qasim Idris da Abdulhaleem Idris a karamar hukumar Ose, Jihar Ondo

Hedkwatar tsaro ta Najeriya, DHQ, tare da tawagar sojoji da DSS sun sake kama wasu yan ta'addan kungiyar ISWAP biyu da ake zargi da kai hari a cocin katolika na St. Francis da ke Owo, Jihar Ondo a ranar 5 ga watan Yunin 2022.

Kara karanta wannan

Sako Mutumin Da Ake Zargin Ya Aikata Laifin Kisan Kai Na Kokarin Tayar Da Tarzoma A Jigawa

Harin Cocin Owo.
An Sake Kama Mutum 2 Cikin Yan Ta'addan Da Suka Kai Hari Cocin Owo
Asali: Original

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Direktan watsa labarai na DHQ, Manjo Janar Jimmy Akpor, cikin wata sanarwa a daren jiya ya ce wadanda ake zargin - Al-Qasim Idris da Abdulhaleem Idris an kama su ne a ranar Talata 9 ga watan Agustan 2022 a Jihar Ondo, rahoton Leadership.

Hakan ya kawo adadin wadanda ake zargin da kai hari a cocin zuwa shida, an kashe kimamin mutane 40 a harin.

Janar Akpor ya ce Abdulhaleem, tare da wasu manyan kwamandojin ISWAP, a baya sun kai hari kan sojoji a Okene, karamar hukumar Okene, Jihar Kogi, hakan ya yi sanadin rasa rayyuka.

Sanarwar ta ce:

"Idan za a iya tunawa CDS Janar Lucky Irabor, yayin ganawarsa da editoci da yan jarida a jiya Talata 9 ga watan Agustan 2022, ya sanar da kama yan ta'adda 4 cikin wadanda suka kai hari cocin St Francis, Owo a ranar 5 ga watan Yunin 2022.

Kara karanta wannan

Yadda Dan Najeriya Ya Badda Kamanni A Matsayin Mace A Facebook, Ya Damfari Dan Indiya Naira Miliyan 31

"An kama su ne yayin atisayen hadin gwiwa na sojoji da DSS a Eika, karamar hukumar Okehi, Jihar Kogi a ranar 1 ga watan Agustan 2022.
"Wadanda aka kama sun hada da Idris Abdulmalik Omeiza (a.k.a Bin Malik), Momoh Otohu Abubakar, Aliyu Yusuf Itopa da Auwal Ishaq Onimisi.
"Awanni bayan bayanin da CDS ya fitar na kama maharan cocin Owon guda hudu, an sake kama yan ta'addan ISWAP biyu, wadanda ke da hannu a harin cocin Omialafara (Omulafa) karamar hukumar Ose, Jihar Ondo a jiya 9 ga watan Agusta.
"An kama su ne sakamakon hadin gwiwa tsakanin sojoji da DSS. Wadanda ake zargin sune Al-Qasim Idris da Abdulhaleem Idris. A sani cewa Abdulhaleem tare da wasu kwamandojin ISWAP, a baya sun kaiwa sojoji hari a Okene, karamar hukumar Okene, Jihar Kogi wanda ya yi sanadin rasa rayyuka."

Shugabannin sojojin da yan sanda da DSS sun sha alwashin cigaba da tare don samar da zaman lafiya da tsaro a dukkan kasa.

Kara karanta wannan

Sace kudin kasa: An soke belin daya daga cikin abokan harkallar tsohon akanta janar

Jerin Sunayen Yan Ta'adda Da Suka Kai Kazamin Harin Cocin Owo Inda Suka Kashe Fiye Da Mutum 30

Tunda farko, hedkwatar Tsaro, ta bakin babban hafsan tsaro, Janar Lucky Irabor a ranar Talata 8 ga watan Agusta ta tabbatarwa yan Najeriya cewa an kama yan ta'addan da suka kai hari a cocin Katolika na Owo, Jihar Ondo.

Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit CDS Irabor, yayin taro da shugabannin kafafen watsa labarai a Abuja ya ce sojoji suna wani atisaye ne suka kama wadanda ake zargin tare da kwato wasu abubuwa daga hannunsu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel