Wata ’Yar Najeriya Ta Bayyana Irin Aikin Wahalar da Ta Ke Tika a Gona a Kasar Waje
- Wata ‘yar Najeriya da ke zaune a kasae waje ta yi bayani game da rayuwa a Turai da abin da take yi domin samun na abin ka a can
- A cikin wani faifan bidiyo da ke yawo a shafukan sada zumunta, matar ta ce zama a Turai ba abu ne mai sauki ba saboda akwai bukatar ba da shawara ga wadanda ke son zuwa
- Sai dai kuma ‘yan Najeriya a shafin sada zumunta sun bukaci matar da ta dawo gida idan har ta gaji da zaman na Turai
Jama'a sun bukaci wata ‘yar Najeriya da ke zaune a kasar waje da ta tattara kayanta ta fara kama hanyar dawowa gida idan zaman Turai ya gundureta.
Shawarar na zuwa ne jim kadan bayan da wani bidiyo ya bayyana a yanar gizo wanda ke nuna matar tana aiki a cikin wata gona.
Turai ba wuri ne mai saukin zama ba, a cewar matar
A cikin faifan bidiyon, an ga matar tana korafin cewa idan da tana rayuwarta a Afirka ne ba za ta yi aikin gona ba.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Ta ci gaba da cewa Turai ba wuri ne mai saukin zama ba kuma masu son kaura daga Afrika zuwa turai ya kamata a sanar da su yadda rayuwa take a can domin rage yiwa rogo kallon kitse.
Sai dai, wasu 'yan Najeriya a shafin Instagram da aka yada bidiyon ba su daukin batun da sauki ba, inda suka ba ta shawarin ta tattara ta dawo Najeriya
Wasu daga cikinsu ma sun zarge ta da tafka karya, suna masu cewa tana kokarin hana wasu zuwa Turai su more ne.
Kalli bidiyon:
Yan Najeriya a Instagram sun mayar da martani
@danny_yhunq ya ce:
"Ki dawo mana."
@officialabnice ya mayar da martani da cewa:
"Ba sauki mana, dawo Najeriya kawai.....Tunda ita Najeriyar da sauki."
@mrsmile_commedian ya ce:
"Ina fatan ba dai karya kike sharara mana ba."
@naomikamara92 ya ce:
"Ki dawo ni kuma in dauki matsayinki,.."
@yemartforever ya ce:
"Inda kika yanke shawarar zama kenan 'yar uwa ta."
@tola_leena ya ce:
"Amma ai kudin da ake samu ya wuce na nan, kar ki mana karya."
Yadda Wani Mutum ya Dawo Daga Kasar Waje, ya Tarar An Fara Gini a Filinsa
A wani labarin kuma, wani jami'in diflomasiyya kuma marubuci dan kasar Zambia Anthony Mukwita, ya dawo kasarsa kwanan nan bayan ya kwashe kusan shekaru goma yana tangaririya a kasashen waje.
Mukwita ya kasance mataimakin jakada a ofishin jakadancin Zambia dake birnin Stockholm na kasar Sweden, inda ya rayu tare da matarsa Elaine da 'ya'yansa biyu Lubinda da Lushomo.
Yayin da ya dawo gida lokacin Kirsimeti, ya dumfari inda filinsa yake, amma sai ya ga wani abin ban mamaki.
Asali: Legit.ng