Yadda Wani Mutum ya Dawo Daga Kasar Waje, ya Tarar An Fara Gini a Filinsa

Yadda Wani Mutum ya Dawo Daga Kasar Waje, ya Tarar An Fara Gini a Filinsa

  • Wani dan jarida dan kasar Zambia Anthony Mukwita ya shiga wani gida da wani wanda bai sani bay a gina a kan filinsa
  • Jami’in diflomasiyyar ya bayyana hakan ne a shafinsa na Facebook, inda ya bayyana cewa ya shafe kusan shekaru 10 baya kasar kwata-kwata
  • Mutane a shafukan sada zumunta sun ce masa ya nemo mutumin da ya yi ginin ya sayar masa da filin domin kowa ya samu ribar kudin da ya zuba

Wani jami'in diflomasiyya kuma marubuci dan kasar Zambia Anthony Mukwita, ya dawo kasarsa kwanan nan bayan ya kwashe kusan shekaru goma yana tangaririya a kasashen waje.

Mukwita ya kasance mataimakin jakada a ofishin jakadancin Zambia dake birnin Stockholm na kasar Sweden, inda ya rayu tare da matarsa Elaine da 'ya'yansa biyu Lubinda da Lushomo.

Kara karanta wannan

Sai Da Na Gargadi Buhari Cewa Zai Lalata Kasar Nan - Khalifa Sanusi

Yadda wani ya gine filin jami'in diflomasiya
Yadda Wani Mutum ya Dawo Daga Kasar Waje, ya Tarar An Fara Gini a Filinsa | Hoto: Anthony Mukwita
Asali: UGC

An kwace masa fili

Yayin da ya dawo gida lokacin Kirsimeti, ya dumfari inda filinsa yake, amma sai ya ga wani abin ban mamaki.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

A bayyane yake cewa, mutumin da ya yi ginin ya yi amfani da rashinsa ne kawai ya kwace filin ya gina gidansa a kai.

Fitaccen dan jaridan na duniya ya ce shi da matarsa Elaine sun sha matukar mamaki a lokacin da suka ziyarci filinsu da ke Kabangwe.

Ya yada a Facebook cewa:

"Wani wayayye ya fara kuma ya kusa kammala ginin gida mai dakuna hudu. Filin yana dauke da sunan mata da ni, me za ku yi?"

Jama’ar intanet sun ba shi shawarar ya sayar da filin

Jama’a a shafin sada zumunta sun shaida wa tsohon manajan daraktan na jaridar Daily Mail ta Zambiya da ya nemo mai ginin ya sayar masa da filin domin kada su biyu su yi asarar kudadensu.

Kara karanta wannan

Yazid Surajo: Matashi 'dan Najeriya Mai Digirin Digir Wanda ya Koma Sana'ar Jari Bola

Wasu, duk da haka, sun bayyana ra'ayin cewa nesa da ya yi da filin na tsawon lokaci ne yasa aka sanya filin a kasuwa har aka siyarwa wani.

Musanga Mushinge:

“Ku daidaita ta hanyar sayar masa da filin a kan farashin da yake yanzu tare da biyanka diyya saboda rashin jin dadi da ya haifar don kada ya rasa kudinsa. Ina muku fatan nasara ku biyun."

Charity Mphande:

"Ka gode wa mutumin da ya yi karimcin fara gina gida a madadin ka. A wani muhimmin batu ko da yake, kawai ku sayar wa da mutumin wannan filin idan kuka la'akari da cewa kuna da wani wuri inda za ku iya farawa."

Dan Najeriya Mafi Tsufa a Raye: An Gano Wani Tsoho Mai Shekaru 126 a Raye Kuma da Karfinsa

A wani labarin, hukumar lafiya ta duniya (WHO) a shekarar 2020 a kididdigar kiwon lafiya ta duniya ta nuna cewa adadin rayuwar 'yan Najeriya ya kan kai 62.6.

Kara karanta wannan

Kar yajin ya kare: Dalibin jami'a aji 3 ya kama sana'a, ya ce sana'arsa ya sa a gaba yanzu

Rahoton ya yi nuni da cewa, tsawon rayuwar namiji dan Najeriya zai iya kai 61.2, yayin da na mace kuwa zai kai 64.1.

Hakan ya nuna cewa Najeriya ce ta samu matsayi na 167 a jerin kasashen da ke cikin rahoto, amma mutum daya ya rushe batun, bayan gano yawan shekarunsa da kuma yadda yake rayuwarsa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel