Bidiyon Wani Dan Kasar Kamaru Da Ya Bayyana Farin cikin Dawowa Najeriya Ya Janyo Cecekuce

Bidiyon Wani Dan Kasar Kamaru Da Ya Bayyana Farin cikin Dawowa Najeriya Ya Janyo Cecekuce

  • Wani dan kasar Kamaru ya bayyana farincikin sa na dawowa kasar Naeriya da zama a soshiyal midiya
  • Matashin dake cike da zumudi ya wallafa wani faifan bidiyo yana daukar tafiyarsa daga Kamaru zuwa Najeriya
  • Matashin yana da kwarin gwiwa game da samun aiki a Najeriya kuma zai yi rayuwa cikin jin dadi

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Jihar Legas - Wani dan kasar Kamaru ya janyo ce-ce-ku-ce a shafukan sada zumunta bayan ya bayyana farinckin sa na dawowar Najeriya da zama. Rahoton Legit.NG

Matashin ya sanar da haka ne a shafin sa na Tiktok @daddyclivert tare da faifan bidiyo ya saka wanda yana nuna shiogwar sa Najeriya.

Ya yiwa Bidiyon nasa taken 'Na gode mu ku duka, da kuka sa hijira na ya yiwu. Ina matukar farin ciki. Ku yi min fatan alheri.

Kamaru
Wani Matashi Ya Bayyana Farin cikin sa Dawowa Najeriya Inda Yace Zai Samu Aiki Yayi Rayuwa Cikin Farin ciki FOTO Legit .NG
Asali: UGC

Bidiyon ya nuna yadda ya isa filin jirgin saman kamaru a cikin mota da yadda ya sauka a jihar Legas.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yan Najeriya da dama sun bayyana mamakin su game da matakin da ya dauka, amma shi ya nuna ya ji dadin sa matuka.

Ga Martanin Yan Najeriya Ga Sakon Faifon Bidyon da Matashin ya saka

Da yake mayar da martani ga wani da ya mishi tambaya a shafin sa inda ya ce masa ko yana da yan uwa da za su tallafa masa a Najeriya, matashin ya bayyana cewa yana da isassun kudi a wurinsa da zai fara rayuwar sa da su Najeriya.

Wani Mai suna Glowing, ya ce Najeriya na cike da 'yanci da jin dadi, idan ba don rashin gwamnati ba, da Najeriya ta kasance kasa mafi kyau a duniya. Barka da zuwa kasata ina maka addu'a da fatan alheri.

olivetta_chantal2341 ya ce Zai dawo nan ba da jimawa ya in kasance tare da su da zarar peter obi ya zama shugaban kasa. yana fatan haduwa da su idan ya dawo, yayi kewar kasar sa kamar hauka.

Chukwuemeka DjPrinzy, ya ce masa kada ya zauna Legas, ya tafi Abuja saboda babu kwanciyar hankali a Legas.

Nancy tace masa, yayi alkawarin zama da mu a lokacin zaman lafiya da lokacin rashin zaman lafiya ?bayan haka tana masa fatan alheri .

Yan Takara Biyar Da Suke Kan gaba Wajen Neman Kujerar Masari

A wani labari kuma, Yan takarar gwamna 13 ne suka fito takara a zaben badi a jihar Katsina, bayan zaben fidda gwani na jam’iyyun siyasa daban-daban.

Amma, biyar ne kawai daga cikinsu ake ganin za su yi fice a zaben. Rahoton The Nation

Asali: Legit.ng

Online view pixel