Yazid Surajo: Matashi 'dan Najeriya Mai Digirin Digir Wanda ya Koma Sana'ar Jari Bola

Yazid Surajo: Matashi 'dan Najeriya Mai Digirin Digir Wanda ya Koma Sana'ar Jari Bola

  • Matashi Yazid Surajo 'dan asalin Karofi a Dutsinma ta jihar Katsina wanda ya kama sana'ar jari bola duk da digirin digir da yake da shi
  • A cewar matashin, ya nemi aiki amma bai samu, lamarin da yasa ya kama wannan sana'ar kuma yake samun abubuwan bukata na rayuwa
  • Yazid yayi tsokaci tare da wallafa hotunan shaidar kammala karatuttukansa, yace gara ya mutu a tsaye da ya raya a durkushe kan guiwoyinsa

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Katsina - An haife shi kuma ya girma a garin Karofi na karamar hukumar Dutsinma ta jihar Katsina, Yazid wanda ke da digirin digir daga jami'ar Bayero dake Kano yanzu ya koma sana'ar jari bola a Legas.

Surajo yayi karatun sa na firamare a Karofi Model Primary School daga 1996 zuwa 2002. Daga nan ya wuce GGSS Karofi daga 2002 zuwa 2008, jaridar Daily Trust ta bayyana a tattaunawa da tayi da shi.

Kara karanta wannan

Tsigaggen sarki Sanusi ga matasa: Ku gina Najeriya, ku daina guduwa kasashen waje

Yazid Surajo
Yazid Surajo: Matashi 'dan Najeriya Mai Digirin Digir Wanda ya Koma Sana'ar Jari Bola. Hoto daga Yazid Surajo
Asali: Facebook

A 2010, ya samu gurbin karatu a jami'ar Umar Musa Yar'adua dake Katsina inda ya karanci tarihi.

Sai dai, ya yayin da yake makaranta, Surajo ya rasa mahaifinsa wanda sifetan 'dan sanda ne a 2010. Rayuwa tayi tsanani domin kuwa iyalan sun dinga kokarin ganin sun samu kudaden da ya dace gwamnati ta biya su na mutuwar mahaifinsu.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kamar yadda Surajo yace, sun kwashe shekaru 10 kafin hukumar 'yan sanda sun saki N3.5 miliyan ga iyalan, wanda rabin kudin da ya kamata a basu kenan.

"Mun sha wahala wurin ganin mun karbo kudin mahaifinmu a kan lokaci saboda tsananin rayuwa da muka shiga. Wasu jami'ai sun damfare mu kafin mu samu kudin daga bisani," Surajo ya koka.

Rayuwa bayan makaranta

Bayan kammala digirinsa na farko da hidimar kasa a Osun, Surajo ya fara tunanin matakin gaba da zai dauka na rayuwarsa.

Kara karanta wannan

Kar yajin ya kare: Dalibin jami'a aji 3 ya kama sana'a, ya ce sana'arsa ya sa a gaba yanzu

Cike da sa'a, sai ya samu N-Power karkashin shirin NSIP inda ake biyansa N30,000.

Bayan ya kammala shirin, Surajo ya koma Legas neman aiki. Bayan neman ayyukan gwamnati ya rasa, matashin ya yanke shawarar fara jari bola.

Yace:

"A bayyane yake, idan kana son samun abun arziki a rayuwa, a kalla sai ka fara da sadaukarwa. A lokacin da na kammala hidimar kasa a 2016, na yanke shawarar ba zan yi zaman banza ba.
"Da yawa daga cikin abokaina su kan je Legas, nima ban yi kasa a guiwa ba na bi su. Wasu sun ce ban dace da kasuwancin ba saboda yana bukatar karfi. Wadanda suka sanni da halayyata sun san zan iya jure kalubalen da zan tsinci kaina a ciki."

Yadda kasuwancin jari bola ke aiki

Surajo ya ce shi da wasu mutum sun kai 70 suke aiki karkashin wani mai suna Dandogo. Dandogo na samar musu da kudi kullum inda suke zagaya gari don samun karafunan da zasu siya.

Kara karanta wannan

Yajin ASUU: Yadda dalibin jami'a ya kama sana'ar siyar da shayi don yakar zaman kashe wando

Yace:

"Wasu ana basu N7,000 wasu N10,00 har zuwa N30,000, ya danganta da yawan da ake so. Bayan karbar kudin, kowa zai dauka akori kurarsa ya fara turawa yana neman karafuna.
"Idan ka samu ka siya wanda bai wuce kudinka ba. Ka kira a sake turo maka kudi har zuwa yamma. Kowa sai ya koma da abinda ya samu, a auna a biya shi kudin aikinsa. Haka muke yi a kowacce rana."

Komawa makaranta don yin digirin digir

A 2018, Surajo ya samu gurbin karatun digirin digi da jami'ar Bayero dake Kano.

Biyan kudin makaranta ya zame masa alakakai. Sai da ya siyar da filinsa sannan ya dage ya kammala karatun.

Tsarin Surajo na gaba

Surajo yace yana da tsarikan zamanantar da sana'ar jari bola idan ya samu jarin da yake bukata.

A kalamansa:

"Zan yi rijistar kamfaninsa kuma in yi wa ma'aikatana rijista. Zan wayar musu da kai a kan irin kayayyaki da ya dace su siya da kuma inda ya dace su samo.

Kara karanta wannan

An Cafke Mutumin Da Ya Kai Yan Mata Otel, Ya Sace Musu iPhone 6 Bayan Zuba Musu Maganin Barci Cikin Abin Sha

"Zan kuma yi amfani da soshiyal midiya wurin kira ga matasa da su zama masu dogaro da kansu ta hanyar kasuwanci. Ina shawartarsu da su gujewa saka kansu cikin ayyukan laifi kamar damfarar yanar gizo, fashi da makami, garkuwa da mutane da sauransu."

A shafinsa na Facebook, Surajo ya wallafa hoton kansayana dauke da wasu karafunan jari bola da kuma shaidar kammala karatuttukansa.

"Gara ka mutu a tsaye da ka rayu a kan guiwoyinka. Gara in yi datti amma in cika cikina da in yi fes ina fama da yunwa. Godiya ga kasar da ba a amfani da masu ilimi yadda ya dace"

Asali: Legit.ng

Online view pixel