Jarumi Kabiru Nakwango Ya Musanta Rade-radin Mutuwarsa da Ake Yadawa

Jarumi Kabiru Nakwango Ya Musanta Rade-radin Mutuwarsa da Ake Yadawa

  • Fitaccen jarumin fina-finan Kannywood, Kabiru Nakwango, ya musanta rade-radin mutuwarsa dake ta yawo a soshiyal midiya
  • An fara yada rade-radin ne a ranakun Litinin da Talata inda ake cewa ya rasu a ranar Lahadi, lamarin da ya musanta da bidiyonsa inda yake gona
  • An ga jarumin rike da fatanya a gona inda yake sanar da masoyansa cewa yana nan da ransa kuma cike da koshin lafiya

Kano - Fitaccen jarumin Kannywood, Kabiru Nakwango, ya musanta rade-radin mutuwarsa da ke ta yawo a soshiyal midiya tsakanin ranar Litinin zuwa safiyar Talata.

Nakwango, wanda yake yawan fitowa a matsayin uba a fina-finan, an fara yada cewa ya mutu a ranar Lahadi.

A yayin musanta rade-radin, tsohon jarumin yace yana nan da ran shi da lafiya.

Kara karanta wannan

Sai Da Na Gargadi Buhari Cewa Zai Lalata Kasar Nan - Khalifa Sanusi

Kabiru Nakwango
Jarumi Kabiru Nakwango Ya Musanta Rade-radin Mutuwarsa da Ake Yadawa. Hoto daga Premiumtimesng.com
Asali: UGC
A wani gajeren bidiyo da yayi a gonarsa, Nakwango ya rike fatanya yayin da yake amsa waya kuma yake cewa, "Dukkan masoyana su sani cewa ina cikin koshin lafiya kuma a raye. Gani nan a gonata ina aiki."

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Hakazalika, abokinsa aikinsa kuma furodusa Abba Almustapha, ya musanta rade-radin a shafinsa na Instagram inda yace, "Yanzu nayi magana da Nakwango kuma ya sanar da ni cewa yana gona yanzu haka. Bai rasu ba kamar yadda ake ta ruwaitowa a soshiyal midiya."

Waye jarumi Kabiru Nakwango?

Nakwango ya fito a manyan fina-finan Kannywood da suka hada da Kukan Kurciya.

Fitaccen jarumin ya shiga masana'antar yana matashi tare da kungiyar dirama ta Fuskar Arewa a 1973 inda kungiyar ta watse a 1975.

Daga nan ya shiga kungiyar Sardauna Youth and Drama Association daga 1987 zuwa 1994.

Kara karanta wannan

Bidiyo: Mai siyar da tsire ya zama ɗan gaye bayan kamfani sun ɗauke shi talla

Jarumin ne ya samar da kungiyar Dabo Films Association, kungiyar da ta samar da wasu daga cikin ingantattun diramomi a arewacin Najeriya.

Bidiyo: Matashin Dake Kaunar Jaruma Maryam Yahaya, Yake Fatan su Mutu Rana Daya

A wani labari na daban, bidiyon wani matashi wanda ke bayyana zunzurutun kaunarsa ga jarumar fina-finan Kannywood, Maryam Yahaya, ya bai wa jama'a mamaki.

A bidiyon da @kannywoodcelebrities.ng suka wallafa a Instagram, an ga matashin yana bayyana tsantsar kaunarsa ga matashiyar jarumar mai tashe.

Matashin da har a yanzu ba a gano sunan shi ba, yace ba zai iya rayuwa babu jaruma Maryam Yahaya a karkashin inuwar sa ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng