Jerin Sunayen Yan Ta'adda 5 Da Suka Kai Kazamin Harin Cocin Owo Inda Suka Kashe Fiye Da Mutum 30
Hedkwatar Tsaro, ta bakin babban hafsan tsaro, Janar Lucky Irabor a ranar Talata 8 ga watan Agusta ta tabbatarwa yan Najeriya cewa an kama yan ta'addan da suka kai hari a cocin Katolika na Owo, Jihar Ondo.
ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit
CDS Irabor, yayin taro da shugabannin kafafen watsa labarai a Abuja ya ce sojoji suna wani atisaye ne suka kama wadanda ake zargin tare da kwato wasu abubuwa daga hannunsu.
Shugaban sojin ya ce ana cigaba da bincike domin gano sauran yan ta'addan da suka boye.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Kalamansa:
"Game da harin Owo, mun gano motar karshe da yan ta'addan suka yi amfani da shi mun kuma kama wasu tare da kwato wasu abubuwa masu muhimmanci da muke aiki a kai.
"An kama wasu mutane dangane da harin na Owo da kwato kayayyaki. A ranar, mun bi su zuwa wani wuri mun kwato motarsu kuma muna cigaba da bibiyarsu. Mun fada muku sai mun gano su, ina iya tabbatar maka cewa za a hukunta maharan da masu daukan nauyinsu."
Ya bada suna wasu daga cikin wadanda aka riga aka kama:
1. Momoh Ojo Abubakar
2. Aliyu Yusuf Itokpka
3. Auwal Ishaq Onimisi
4. Idris Ojo
5. Idris Abdulmalik Omeiza (daya daga cikin wadanda suka kitsa harin)
Harin Cocin Owo: Gwamna Akerdolu ya tabbatar da kama mutum 5 da ake zargi
A bangarensa, gwamnan Jihar Ondo, Rotimi Akeredolu, a ranar Talata ya tabbatar da kama yan ta'addan.
Gwamna Akeredolu ya ce:
"Ina iya tabbatar da abin da CDS ya ce. An kama su makon da ta gabata an kuma tura min hotunan wadanda ake zargin.
"An kama kimanin biyar cikinsu yayin da ake bibiyar sahun sauran."
Dogo Nabajallah: Ƙasurgumin Ɗan Bindigan Katsina Ya Gamu Da Ajalinsa Sakamakon Rikicin Neman Aure
A wani labarin daban, rikici ya barke tsakanin bangarorin ƴan bindiga biyu masu adawa da juna a Katsina wadda ya yi sanadin mutuwar shugaban yan bindiga, Nabajallah, da wasu yan bindigan uku, rahoton The Punch.
Majiyoyi sun ce an kashe shugaban yan bindiga, Dogo Nabajallah a cikin dajin Dungun Muazu da ke karamar hukumar Sabuwa a ranar Laraba.
A cewar rahoton Premium Times Hausa wasu ƴan bindigan da ke adawa da shi ne suka afka masa suka kashe shi saboda rikicin neman aure da ke tsakanin yaronsa da bangaren su yan adawan.
Asali: Legit.ng