Dan Najeriya Mafi Tsufa a Raye: An Gano Wani Tsoho Mai Shekaru 126 a Raye Kuma da Karfinsa
- Yayin da wasu kasashe ke ganin rayuwar 'yan Najeriya bata cika tsawo ba idan aka kwatanta da wasu, wani dattijo ya ba da mamaki
- Legit.ng Hausa ta gano wani tsoho mai shekaru 126, kuma an gano lafiyarsa lau fiye da yadda ake tsammani ga mai irin shekarunsa
- Wani matashi ya bayyana tarihin wannan tsoho, ya kuma naqalto abubuwa masu ban mamaki game da shi
ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit
Jihar Imo - Hukumar lafiya ta duniya (WHO) a shekarar 2020 a kididdigar kiwon lafiya ta duniya ta nuna cewa adadin rayuwar 'yan Najeriya ya kan kai 62.6.
Rahoton ya yi nuni da cewa, tsawon rayuwar namiji dan Najeriya zai iya kai 61.2, yayin da na mace kuwa zai kai 64.1.
Hakan ya nuna cewa Najeriya ce ta samu matsayi na 167 a jerin kasashen da ke cikin rahoto, amma mutum daya ya rushe batun, bayan gano yawan shekarunsa da kuma yadda yake rayuwarsa.
Yadda aka gano Luke Ahama Nwachukwu
Mista Luke Ahama Nwachukwu wanda aka fi sani da Oshimili a halin yanzu yana da shekaru 126 kuma ba wai kawai yana raye ba, har ma karfi gare shi a wannan shekarun.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Legit.ng ta samu labarin cewa, mutumin dan asalin jihar Imo ne bayan da jikan sa, Mista Ephraim N. Nwachukwu ya nuna shi shi a shafinsa na LinkedIn.
A Satumban 2021, Ifraimu ya yada bidiyo a LinkedIn na kakan nasa yana sare itace da adda ba tare da taimakon wani ba.
Matashin ya kuma bayyana cewa kakansa, wanda mai sana'ar rufin gida ne na gargajiya, har yanzu yana da karfin gaske har ma ya kan hau keke da kansa. Ya kara da cewa tsohon dan kokawa ne tun yana karami kuma bai taba cutar kowa ba.
Ya sahihancin labarin?
Legit.ng ta tuntubi Ephraim domin sanin sahihancin labarin wannan dattijo kuma hakan ya tabbata.
A wata hira ta wayar tarho da wakilin Legit.ng mai suna Victor Duru, Luke wanda yayi magana cikin harshen Igbo ya tabbatar da cewa yanzu shekarunsa 126 a duniya.
Mutumin dan asalin yankin Aboh Mbaise a Imo ya bayyana cewa abin takaici bai san inda takardar shaidar haihuwarsa take ba balle ya ba Legit.ng ta tabbatar.
Lokacin da aka tambaye shi ko ya taba tunanin zai yi rayuwa mai tsawo, sai ya ce:
"Idan da za ku tambaya a baya, zan ce ba zan yarda zan kai har wannan lokacin ba, don haka ban yi tunanin haka ba."
Legit.ng ta samu labarin cewa matarsa tana raye. Tsohuwar mai suna Cyrena Nwachukwu ta auri Luke ne tun tana karama amma ta kasa bayyana ainihin shekarunta.
A Ci Gaba da Yi: Dalibin Jami’a Ya Kama Sana’a, Ya Ce ASUU Su Tabbata Suna Yaji Kawai
A wani labarin, Abdulhadi Dankama ya samu shiga sashen ilmin lissafi a jami'ar Bayero ta jihar Kano domin yin digirinsa na farko.
Ya kamata Dankama ya kammala digirinsa a yanzu idan da yajin aikin da kungiyar malaman jami’o’i ta fara ba kan rashin jituwa da gwamnatin tarayya bata shafe shi ba.
Za ku yi tunanin Dankama wanda a yanzu yana aji 3 zai kosa ya koma makaranta domin ya gaggauta kammala karatunsa.
Asali: Legit.ng