Sojoji Sun Kama Yan Ta'adda Da Suka Kai Harin Cocin Owo, An Bayyana Sunan Wanda Ya Kitsa Harin
- Rundunar sojojin najeriya ta kama wasu yan ta'adda da suka kai hari cocin Katolika na St. Francis a Owo jihar Ondo
- Babban hafsan tsaro na kasa, CDS, Janar Lucky Irabor ya tabbatar da hakan a ranar Talata 8 ga watan Agusta a Abuja
- CDS Irabor, yayin ganawarsa da shugabannin kafafen watsa labarai a Abuja, ya ambaci wani Idris Abdulmalik Omeiza a matsayin wanda ya kitsa harin
FCT Abuja - Hedkwatar Tsaro ta kasa, DHQ, ta ce ta kama yan ta'addan da suka kai hari a cocin St Francis Catholic Church a Owo, Jihar Ondo, rahoton The Nation.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Babban hafsan tsaro, Janar Lucky Irabor, wanda ya bada sanarwar yayin taro da shugabannin kafafen watsa labarai a hedkwatar tsaro a Abuja ya ce an kama bata garin ne tare da hadin kan hukumomin tsaro.
Yan ta'addan sun kai hari ne a cocin na Katolika a ranar Lahadi kuma suka bude wuta kan masu ibadan suka kashe fiye da mutane 30.
Lamarin ya faru ne a ranar 5 ga watan Yunin 2022.
An ambaci sunan daya cikin wadanda suka kitsa kai harin
Yayin zaman da ya yi da shugabanin kafafen watsa labarai, CDS Iraboh ya bayyana cewa daya cikin wadanda suka kitsa kai harin shine Idris Abdulmalik Omeiza.
Ya ce:
"Omeiza na daya cikin wadanda suka kitsa kai harin ranar 5 ga watan Yuni a cocin Katolika da ke Owo da harin ofoshin yan sanda na karamar hukumar Adavi a Jihar Kogi da ta yi sanadin kisar dan sanda da sace makamai".
CDS din ya kara da cewa an kama Omeiza ne a ranar 1 ga watan Agusta a Eka Okehi a Jihar Kogi yayin wani atisaye da sojoji tare da wasu hukumomin tsaro.
Da zafi-zafi: Sojoji sun gano dan ta'addan da ya kitsa kai hari kan tawagar Buhari a Daura, sun sheke shi
Da ya ke bayyana Omeiza a matsayin "daya cikin manyan yan ta'addan ISWAP da suka tsere daga gidan yarin Kuje" Irabor ya kara da cewa:
"Idris Ojo bai kammala muggan ayyukansa ba domin yana shirin kai wasu muggan hare-haren tare da abokan harkallarsa kafin a kama shi."
Wani rahoto daga Punch ta ambato yana cewa:
"Bayan ganawar da muka yi na karshe, mun samu manyan nasarori. Ina son sanar da ku cewa miyagu sun kai hare-hare da suka hada da harin jirgin kasa, harin gidan yarin Kuje da harin da aka kaiwa tawagar motoccin shugaban kasa.
"Kazalika, harin Owo da aka kai da nufin nuna cewa ba tsaro a kasar. Mun yi nasarar kama wadanda suka kai harin na Owo.
"Ina son gabatar da su ga al'umma, amma ba a kammala bincike ba, sai na canja ra'ayi na. Nan gaba, duniya za ta san cewa sune suka kai harin da wasu hare-hare a kasar."
An Kama Matar Ɗan Bindiga a Katsina Da N2.4m, Mijin Ya Tsere Ya Bar Ta
A wani labarin, yan sanda a jihar Katsina sun kama wata matar aure, Aisha Nura, mai shekaru 27 dauke da kudi Naira miliyan 2.4 na cinikin makamai da aka sayarwa yan bindiga, The Punch ta ruwaito.
An kama Aisha, da aka ce matar dan bindiga ne, a ranar 25 ga watan Yuli a yayin da ta ke shirin hawa kan babur din haya (acaba) daga Batsari zuwa kauyen Nahuta.
Mai magana da yawun yan sandan jihar Katsina, SP Gambo Isah, ya tabbatar da hakan a ranar Juma'a.
Asali: Legit.ng