Fitaccen Malamin Addinin Islama Gumi Ya Damu da Yadda Babu Adalci a Najeriya
- An yi taron samar da zaman lafiya a Borno, an tattauna tare da wayar da kan tsofaffin 'yan Boko Haram da suka tuba
- Sheikh Ahmad Gumi ya yi tsokaci game da halin da ake ciki a Najeriya, ya ce sam babu adalci ne a kasar shi yasa ake shan wahala
- Wani fitaccen Bishap a jihar Borno karkashin CAN ya yi tsokaci game da shugaban da ya kamata a zaba a 2023
Maiduguri, jihar Borno - Shahararren malamin addinin Musulunci, Sheikh Ahmad Gumi ya soki shugabancin siyasa a Najeriya, yana mai cewa al'ummar kasar na da raunin tsarin adalci, Channels Tv ta ruwaito.
Gumi ya bayyana hakan ne a lokacin da yake jawabi a wajen taron samar da zaman lafiya da aka shirya a Maiduguri a wani bangare na shirye-shiryen mayar da tsoffin mayakan Boko Haram cikin al’umma.
A cewar malamin:
"Duk wanda ke da wata bukata a kasarmu, mun samar masa da sojoji da zai iya amfani dasu.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
“To me ya sa muke barin ‘ya’yanmu babu karatu? Me yasa ilimi ya zama ba na kowa bane? Me ya sa muke barin al'ummarmu cikin talauci?
“Wasu ‘yan Najeriya na hawa jiragen sama masu zaman kansu yayin da wasu ‘yan Najeriya ba su san inda za su saka ‘ya’yansu a makaranta ba.
"Akwai rashin adalci na zamantakewa. Idan ka je tsarin kotu, adalci babu shi. An rushe tsarin iko. Don haka yara suna can kowa zai iya amfani da su.”
Tikitin Musulmi-Musulmi
Shugaban kungiyar Kiristoci ta Najeriya (CAN) a Borno, Bishop Mohammed Naga shi ma ya halarci taron.
Ya caccaki wadanda suka soki tikitin takarar shugaban kasa na Musulmi da Musulmi na jam’iyyar APC a zaben 2023.
Bishop Naga yace Kiristocin Najeriya ba sa amfana da Shugaba Kirista.
A cewarsa:
“A yanzu Musulmi ne ke mulki, me muke amfana dashi? Muna neman mai ceto ne, mutumin da zai fitar da mu daga matsalolin da muke ciki a kasarsa.”
Ga dai wani bidiyo da kafar ta Channels Tv ta yada lokacin da Gumi da Naga ke magana a wajen taron.
Rashin Tsaro: Gumi Ya Ragargaji Gwamnatin Najeriya Kan Barazanar Hukunta BBC Da Aminiya
A wani labarin, Shahararren malamin addinin musulunci, Sheikh Ahmad Gumi, ya soki gwamnatin tarayya kan barazanar da ta yi na hukunta kafafen watsa labarai game da wallafa rahotanni kan rashin tsaro da ya dade yana damun kasar, rahoton Channels TV.
A ranar Alhamis, Ministan Labarai da Al'addu, Lai Mohammed ya ce za a hukunta BBC da Trust TV saboda bidiyo da suka yi na yan bindiga.
Amma, a martaninsa, malamin addinin musuluncin ya ce gwamnati na kokarin rufe bakin kafafen watsa labarai su dena bayyana gazawarta da kawar da hankulan mutane daga rashawa na kashe kudi a bangaren tsaro.
Asali: Legit.ng