NDLEA Sun Yi Ram da Fasto, Ana Zarginsa da Shigo da Kwayoyi daga Kasar waje

NDLEA Sun Yi Ram da Fasto, Ana Zarginsa da Shigo da Kwayoyi daga Kasar waje

  • Dakarun hukumar NDLEA sun kama wani Fasto Anietie Okon Effiong da hannu a harkar kwaya
  • Ana zargin Anietie Okon Effiong da laifin shigo da kilo 90 na kwayar Mkpuru Mmiri daga Indiya
  • NDLEA ta kuma yi nasarar cafke masu safarar kwayoyi a yankunan Legas, Kaduna da Sokoto

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

FCT, Abuja – Fasto Anietie Okon Effiong wanda ake zargin gawurtaccen mai safarar kwayoyi ne, ya fada hannun jami’arn hukumar NDLEA.

Jawabin da ya fito daga bakin mai magana da yawun bakin NDLEA, Femi Babafemi a ranar Lahadi 17 ga watan Agusta 2022 ya tabbatar da haka.

Sanarwar tace an kama Anietie Okon Effiong dauke da ganguna uku na kwayar methamphetamine wanda aka fi sani da Mkpuru Mmiri.

Legit.ng ta rahoto NDLEA ta na zargin an shigo da kwayoyin na Mkpuru Mmiri ne daga Indiya.

Rahoton ya nuna cewa an yi nasarar cafke kayan masu nauyin kilo 90 a wata motar haya mai lamba RSH 691XC a garin Ojuelegba da ke jihar Legas.

Jami’an NDLEA sun tare wannan motar a hanyar Umuahia-Ikot Ekpene a ranar Asabar da ta gabata a lokacin da aka tsaida motoci, ana lalube.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kamen NDLEA
Wadanda NDLEA ta kama Hoto: NDLEA
Asali: Facebook

Za a fita da su daga Najeriya

Kowace ganga tana cin kilo 30 da za a kai wa Fasto Anietie Okon Effiong, wanda shi ma dakarun hukumar suka yi ram da shi yana shakatawa a Oron.

Kakakin NDLEA yace an shirya za a kai kwayoyin kasar Kamaru ne a lokacin da aka tare motar.

An tare kwayoyi a wasu jihohi

A cewar Femi Babafemi, NDLEA ta karbe tulin Mkpuru Mmiri ne a lokacin da aka tare wasu kwayoyin da aka shirya za a fita da su kasashen ketare.

An yi nufin kai tabar wiwin da wasu kwayoyin ne zuwa kasashen Australia, Indonesia da Philippines da kuma birnin Dubai a United Arab Emirates.

An boye kwayoyin ne a cikin robobin mai, duwatsun guga da wasu kayan adon mata. Bayan nan an yi wasu kamen a jihohin Kaduna, Sokoto, Kogi da Enugu.

Ba yau aka fara ba

Kwanakin baya an ji labarin yada jami’an NDLEA suka yi nasarar kama Ugochukwu Emmanuel Ekwem dauke da kayan shaye-shaye a filin jirgin Legas.

An cafke Rabaren Ugochukwu Emmanuel Ekwem ne a filin tashin jirgin saman MMIA, ya boye wiwi a jikinsa, ya na mai shirin fita da su zuwa Kenya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel