Duk da tsige ni, ba zan kame baki na game da Najeriya, tsigaggen sarkin Kano Sanusi
- Tsohon Sarkin Kano, Sanusi Lamido Sanusi ya bayyana cewa yawancin maganganunsa da ke jawo masa matsaloli sun gama bayyana ayanzu
- Sanusi ya kara da cewa idan har zai zaba tsakanin ka’idojinsa da yin mulki, ba zai saryar da ka’idojinsa don kawai ya samu mulki ba
- Tsohon sarkin ya bayyana haka ne a wani wasan kwaikwayo mai taken, “Emir Sanusi: Truth in Time” a Abuja a ranar Asabar, 6 ga watan Agusta
ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit
FCT, Abuja - Tsohon Sarkin Kano, Sanusi Lamido Sanusi, ya bayyana kwarin gwiwar ci gaba da magana kan karewa da sake gina fasalin Najeriya.
Kamar yadda jaridar The Nation ta ruwaito, Sarkin ya ce galibin maganganunsa da suka jawo masa matsaloli a baya sun zo kuma mutane sun gani.
Tsohon Sarkin wanda yanzu shi ne Khalifan Darikar Tijjaniyyah ta Najeriya ya bayyana haka ne a Abuja a ranar Asabar 6 ga watan Agusta a wani wasan kwaikwayo mai taken “Emir Sanusi: Truth in Time” da aka shirya.
Muna da dadadden tarihin hidima ga Najeriya, cewar Sanusi
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Sanusi ya ci gaba da cewa, yana da gogewa da duk wani abu da ake bukata don bayar da gudunmawa ga gina kasa saboda dadewa da ya yi a yiwa kasar hidima.
Ya jaddada cewa mahaifinsa da ma danginsa, sun dade da yi wa Najeriya hidima, inda ya tuna cewa mahaifinsa shi ne darakta-janar na farko na hukumar leken asiri ta Najeriya (NIA), tun kafa hukumar a 1960.
Sanusi ya ci gaba da cewa idan har za a ba shi zabi tsakanin sadaukar sadaukar ka'idojinsa da kuma rike mukaminsa, ba zai taba sadaukar da ka’idojinsa ba, rahoton Premium Times.
Yace:
“Abubuwan da na ce za su faru, wadanda suka jawo mini matsala, sun faru.
"Zan ci gaba da magana da bayyana ra'ayina, zan ci gaba da kare kasar nan."
Ganduje da Sanusi sun hadu a filin jirgin sama, shekaru 2 bayan da ya tsige shi daga sarauta
A wani labarin, gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje da tsohon sarkin Kano, Khalifa Muhammadu Sanusi II, sun ci karo da juna a filin sauka da tashin jiragen sama na Nnamdi Azikiwe dake Abuja a ranar Litinin.
Wannan ne karo na farko da suka ci karo da juna kuma aka gansu tare tun bayan da gwamna Ganduje ya tube wa Sanusi rawani a 2020.
Gwamnan ya tube rawanin basaraken a ranar 9 ga watan Maris din 2020, kan abinda ya kwatanta da rashin biyayya ga dokoki daga ofishin gwamnan.
Asali: Legit.ng