Za a Gurfanar da Dansandan Da Ya yiwa Wani Mutum Duka da Adda A Fuska

Za a Gurfanar da Dansandan Da Ya yiwa Wani Mutum Duka da Adda A Fuska

  • Babban Sufeto Janar na ‘yan sandan Najeriya ya bayar da umarnin gurfanar da dansandan d aka kama yana yi wa wani mutum bulala a jihar Cross River
  • Dansanda Kofur Okoi Liyomo, ya gana da Babban Sufeto Janar na ‘yan sandan Najeriya Usman Alkali Baba kafin ya fuskanci hukunci
  • Hukumar Yansanda ta gargadi jami'anta da ba zata lamunci duk wani aiki da ya kunshi rashin bin doka da oda ba

Abuja - Babban Sufeto Janar na ‘yan sandan Najeriya, IGP Usman Alkali Baba, ya bayar da umarnin gurfanar da Kofur Okoi Liyomo, dan sandan da aka kama yana yi wa wani mutum bulala a jihar Cross River. Rahoton VANGUARD

Jami’in hulda da jama’a na rundunar, CSP Muyiwa Adejobi ne ya bayyana hakan a wani sako da ya wallafa a shafinsa na Twitter inda ya ce Liyomo ya gana da IGP a Abuja ranar Alhamis kuma zai fuskanci shari’a akan lamarin.

Kara karanta wannan

Buhari Ya Jajantawa Rundunar Yansanda Da Mutanen Jihar Osun Kan Rasuwar Tafa Balogun

okoii
Za a Gurfanar da Dansandan Da Ya yiwa Wani Mutum Duka da Adda A Fuska FOTO LindaIkejiBlog
Asali: UGC

Ku tuna cewa a farkon makon nan ne wani faifan bidiyo na wani dan sanda, da ya yi amfani da gefen Adda yana dukan wani mutum da shi, da aka yi ta yadawa a shafukan sada zumunta wanda hakan ya jawo hankalin manyan jami’an rundunar ‘yan sandan Najeriya.

CSP Muyiwa Adejobi hukumar yansanda NPC ta gargadi jami'anta cewa bazata lamunci duk wani aiki da ya kunshi cin hanci da rashawa, cin zarafi da tayar da zaune tsaye rashin bin doka da oda ba.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Jami’an Amotekun Sun Kara Kama yan Arewacin Najeriya 151 Cunkushe Cikin Tireloli Biyu

A wai labari kuma, Jihar Ondo - Kungiyar tsaro ta kudu maso yammacin Najeriya Amotekun ta sanar da kara kama wasu matasa daga Arewacin Najeriya guda 151. Rahoton BBC

Amotekun ta ce ana zargin matasan da kasancewa 'yan ta'addan dake neman yin kutse da samun mafaka yankin kudu maso yammacin Najeriya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel