Da duminsa: Ganduje da Sanusi sun hadu a filin jirgin sama, shekaru 2 bayan da ya tsige shi daga sarauta

Da duminsa: Ganduje da Sanusi sun hadu a filin jirgin sama, shekaru 2 bayan da ya tsige shi daga sarauta

  • Gwamna Abdullahi Umar Ganduje na jihar Kano, ya ci karo da Khalifa Muhammadu Sanusi II a filin jirgin sama dake Abuja a ranar Litinin
  • Wannan ne karo na farko da gwamnan da tsohon basaraken suka hadu ido da ido tun bayan da gwamnan ya tube masa rawani
  • Gwamna Ganduje ya tube rawanin Sanusi a watan Maris din 2020 inda ya bayyana dalilin hakan da rashin biyayya ga dokoki daga ofishinsa

Gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje da tsohon sarkin Kano, Khalifa Muhammadu Sanusi II, sun ci karo da juna a filin sauka da tashin jiragen sama na Nnamdi Azikiwe dake Abuja a ranar Litinin.

Wannan ne karo na farko da suka ci karo da juna kuma aka gansu tare tun bayan da gwamna Ganduje ya tube wa Sanusi rawani a 2020.

Kara karanta wannan

Bidiyon Bikin Zagayowar Ranar Haihuwar Tsohon Sarkin Kano, Sanusi, An Yanka Kek

Ganduje da Sanusi
Da duminsa: Ganduje da Sanusi sun hadu a flin jirgin sama, shekaru 2 bayan da ya tsige shi daga sarauta
Asali: UGC

Gwamnan ya tube rawanin basaraken a ranar 9 ga watan Maris din 2020, kan abinda ya kwatanta da rashin biyayya ga dokoki daga ofishin gwamnan.

An mayar da Sanusi garin Loko dake jihar Nasarawa daga Kano kuma aka fara bincikar masarautar a yayin da yake sarauta.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Shekara daya bayan nan, gwamnan yace ya yanke hukuncin ne domin bai wa masarautar gargajiyar kariya.

A watan Afirilun 2014, Jonathan ya sauke Sanusi daga kujerar gwamnan babban bankin tarayya bayan tsohon gwamnan bankin ya yi ikirarin cewa wasu mutane karkashin mulkin Jonathan sun sace $49 biliyan.

A yayin ganin laifin fallasar zargin damfarar, Ganduje ya ce tsohon shugaban bankin kamata yayi ya gana da tsohon shugaban kasan wanda ka iya sa a bincika lamarin.

"Jonathan yayi daidai da ya cire Sanusi matsayin gwamnan babban bankin kasar nan, wanda ya kawo masa bakin jini a wasu wurare.

Kara karanta wannan

Gwamnan Arewa ya sa labule da tsohon shugaban kasa Obasanjo kan muhimmin abu

"Lokacin da Sanusi yace $49 biliyan tayi batan dabo a gwamnatin Jonathan, a raina nace a'a, da ka gana da Jonathan a sirrance.
"Da ka bayyana masa abinda ke faruwa daga nan sai ya bincika ta yadda wadanda suka sace kudin ba su riga da sun boye su ba."

Bidiyon Bikin Zagayowar Ranar Haihuwar Tsohon Sarkin Kano, Sanusi, An Yanka Kek

A wani labari na daban, bidiyon bikin zagayowar ranar haihuwar tsohon sarkin Kano, Muhammad Sanusi Lamido ya bayyana a shafukan soshiyal midiya.

A ranar Lahadi, 31 ga watan Yuli ne Sanusi II ya cika shekaru 61 a duniya inda aka yi shagali na musamman domin raya wannan rana.

A cikin bidiyon shagalin wanda shafin hausaa_fulanii ya wallafa a Instagram, an gano tsohon sarkin wanda ake yiwa lakabi da Dawisu sarkin ado tsaye cikin ado da kwalliya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel