Hotuna: Kyawawan jaruman fim mata 3 da suka cafke zukatan zakarun Super Eagle, sun aure su
- Jaruman masana'antun fina-finai a duniya sun saba cafke zukatan mazaje inda har su kan kai ga auren wadanda suka hango su a talabijin
- Akwai wasu jaruman masana'antar fina-finai da suka yi caraf da zukatan fitattun 'yan kwallon kafa na kungiyar Super Eagles inda har suka yi aure
- Daga cikinsu akwai Naja'atu Muhammad, Yetunde Barnabas da Stephanie Oforka wadanda suka auri 'yan wasan kwallon kafa
Soyayya gamon jini ce inji Hausawa. Zakaru kuma 'yan wasan Super Eagles sukan gangara daga duniyar wasanni zuwa daukan abokan rayuwa kyawawa wadanda suka dace dasu kuma su gina iyali.
Wasu daga cikin kwararrun 'yan kwallon kafa sun ci karo ne da soyayya a masana'antun fina-finai inda suka auri kyawawan jarumai.
Ga hotuna da bayanin jarumai mata na fim da suka sace zukatan 'yan kwallon kafa kuma suka shige aka ciki:
1. Kalu Uche and Stephanie Oforka
Tsohuwar sarauniyar kyau kuma jarumar fim, Stephanie Oforka, ta yi shuhura a shekarar 2008 yayin da ta zama wacce ta lashe gasar sarauniyar kyau a Najeriya.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
A 2011, ta auri tsohon zakaran kwallon kafa na Super Eagles, Kalu Uche wanda yayi wa Najeriya wasa tsakanin 2003 zuwa 2012.
2. Olayinka Peters da Yetunde Barnabas
Zakaran kwallon kafa na Slavia Prague, Olayinka, shima kwararren 'dan wasan kwallon kafa na Super Eagles ne wanda a yanzu haka yake auren jarumar fina-finan kudancin Najeriya.
A halin yanzu, zakaran kwallon kafan yana auren fitacciyar jaruma Yetunde Barnabas.
Kyawawan ma'auratan sun yi aure a watan Maris din 2021. Jarumar ta ci gasar kyau ta Najeriya a 2017 kuma an nada ta jakadiyar yawon bude ido a Najeriya a 2019.
Jarumar ta yi suna da fice ne a rawar da ta taka matsayin Miss Pepeye a shirin Papa Ajasco.
3. Shehu Abdullahi da Naja'atu Muhammad
Shehu fitaccen zakaran wasan kwallon kafa na Super Eagles wanda ke auren jarumar Kannywood.
An daura auren masoyan juna Naja'atu Muhammad da Shehu Abdullahi a ranar 18 ga watan Yunin 2021, kwanaki kasan kafin auren Yetunde Barnabas.
Ahmed Musa, kyaftin din Super Eagles ya samu halartar daurin auren.
Ina zan gan shi?: Ahmed Musa ya shirya taimakon tsohon zakaran Olympic dake cike kwararon titi a Legas
A wani labari na daban, kyaftin din kungiyar wasan kwallon kafa ta Najeriya ta Super Eagles, Ahmed Musa, yana son taimakawa tsohon zakaran wasannin Olympic, Bassey Etim, wanda aka gani a yankin Ajah ta jihar Legas yana cike kwazazzaban kan titi.
A baya ana kiran zakaran da 'Iron bar', an gan shi a wani sashin titin Ado/Badore a jihar Legas.
Mawakin Najeriya, Oc Cares, ya bayyana yadda ya ga Bassey na aikin taimakon al'umma a tituna na tsawon lokaci, lamarin da yasa ya neme shi.
Arangamar masoya: Matashin Najeriya ya hadu da baturiyar da suka yi shekaru 2 suna soyewa a yanar gizo
Asali: Legit.ng