Bidiyo: An haska bidiyon Hajiya Dada, mahaifiyar Yaradua tana rera addu'o'i ga Yassine da Shehu a wurin liyafa
- Bidiyon Hajiya Dada, mahaifiyar marigayi shugaba Umaru Musa Yaradua tana addu'o'in fatan zaman lafiya ga jikanta da amaryarsa sun bayyana
- A bidiyon da @fashionseriesng suka wallafa a shafinsu na Instagram, an ga yadda aka haska bidiyon kakar angon a wurin liyafar auren
- An ji tsohuwar mai cike da kamala da nastuwa tana rero addu'o'in fatan zaman lafiya da sabbin ma'auratan kuma masoyan juna
Bidiyon mahaifiyar marigayin tsohon shugaban kasar Najeriya, Alhaji Umaru Musa Yaradua, Hajiya Dada Yaradua, tana jero addu'o"in fatan zaman lafiya ga Shehu 'Yaradua da amaryarsa ya bayyana.
An haska wannan bidiyon ne a majigi yayin da ake tsaka da liyafar auren 'yan gatan, Yassine Sheriff da Shehu Yaradua.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Tsohuwar wacce ta tsufa tukuf an ji tana yi musu fatan alheri da zaman lafiya yayin da zasu shiga sabuwar rayuwar aure.
A bidiyon da @fashionseriesng suka wallafa a shafinsu na Instagram, an ga tsohuwar tana sanye da atamfa a zaune yayin da take addu'o'in.
An kwashe sama da mako daya ana shagalin bikin auren Shehu Umaru Yaradua da amaryarsa Yassine Sheriff wanda aka daura a ranar 23 ga watan Yulin 2022 kuma aka zarce da shagali har zuwa karshen watan Yulin.
Tabbas bikin ya matukar kayatarwa domin ya samu halartar matan manyan kasar nan yayin da Aisha Muhammadu Buhari ta halarci daya daga cikin liyafofin da suka yi.
Kyawawan hotuna da bidiyoyin 'ya'ya da jikokin marigayi shugaba Umaru Musa 'Yaradua a wurin bikin 'dan uwansu
A wani labari na daban, kyawawan hotuna da bidiyoyin 'ya'ya da jikokin tsohon shugaban kasa, marigayi Alhaji Umaru Musa Yar'adu a wurin shagalin auren Shehu Yaradua sun bayyana.
A hotuna da bidiyoyin da aka tattaro da @weddingstreet_ng a Instagram, 'yan uwan angon sun fito shar da su a wurin shagalin auren 'dan uwansu inda suka dinga haskawa tare da walkiya.
Iyalan marigayin tsohon shugaban kasan sun hada da matan tsofaffin gwamnonin Najeriya irinsu Nafisa Shehu Shema, Zainab DakinGari da sauransu.
Asali: Legit.ng