Harin Gidan Yarin Kuje : NSCDC Ta Ba Iyalan Jami’inta Da Aka Kashe N2.8m
- Hukumar Rundunar tsaro ta Jan Kwala NSCDC ta yiwa iyalan jami’anta da aka kashe kyautar Naira miliyan N2.8m
- Shugaban Hukumar NSCDC Ahmed Audi yayi alkwarin daukar diyar jam'in su da aka kashe aiki
- Ahmed Audi yayi kira ga daukacin al'ummar Najeriya da suka rika taimakawa jami'an tsaro da bayyanan da zai taimake su wajen dakile ayyukan yan ta'dda
Abuja - Hukumar Rundunar tsaro ta Jan Kwala NSCDC ta yiwa iyalan jami’anta da aka kashe a lokacin da yan bindiga suka kai hari gidan yarin kuje kyautar makudan kudi da ya kai Naira miliyan biyu da dubu 800 Rahoton Daily.Trust.Aminiya
Kakakin rundunar NSCDC kuma Mataimakin Babban Kwamnada Olusola Odumosu ya fitar da sanarwa a ranar Alhamis a Abuja.
Odumosu ya ce Kwamanda Janar na Rundunar NSCDC, Ahmed Audi mni, ya gabatar da cekin Naira miliyan biyu dari biyar, da kuma kudi a hannu Naira dubu 300 ga matar marigayi Iliyasu da yar sa.
Kwamanda Janar Ahmed Audi mni, ya dau alkawarin baiwa babbar diyar marigayin, Abimiku Abraham, aikin Civil Defence a cikin sabbin ma’aikatan da hukumar zata dauka nan gaba.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A lokacin da yake mika ta’aziyar sa ga iyalan marigayin ya ce hukumar NSCDC za ta cigaba da tuna shi a matsayin mutumin da ya sadaukar da rayuwar sa wajen yiwa kasar sa hidima.
Ahmed Audi, yayi kira sauran kwamandojin rundunar NSCDC na jihohi daba-daban da sauran hukumomin tsaro da su hada kai wajen shawo kan matsalar tsaro da ya addabi kasar.
Ya kuma bukaci sauran daukacin al’ummar Najeriya da su rika taimaka wa jami’an tsaro da bayanai da zai rika taimaka musu wajen dakile ayyukan yan ta’adda.
Mayakan Kungiyar Ansaru na auren Yan mata a Jihar Kaduna
Wani labari kuma, Rahoton dake fitowa daga karamar hukumar Birnin Gwari ta Jihar Kaduna, ya bayyana cewa yan ta’addan kungiyar Ansaru suna auren matan yankin. Rahoton BBC
Labarin Angwancewar wasu mambobin kungiyar da matan garin, ya faru ne a garin Tsohuwar Kuyallo a ranar Talata.
Asali: Legit.ng