Ango ya rasu bayan kwana 12 da aure, bidiyon aurensu da kyakyawar amaryarsa ya taɓa zukata

Ango ya rasu bayan kwana 12 da aure, bidiyon aurensu da kyakyawar amaryarsa ya taɓa zukata

  • Ma'abota amfani da soshiyal midiya sun fara tururuwar aike wa da wata budurwa sakon ta'aziyya bayan mijinta ya rasu kwanaki 12 da aurensu
  • Wani bidiyon kyawawan ma'auratan na auren cocinsu wanda aka yi ranar 28 ga watan Mayu ya matukar birge jama'a amma ya taba zukata
  • An yi auren cocin ne bayan kwanaki biyu da yin auren gargajiya, ashe basu san cewa mai rabawa ta kusa raba su ba gaba-daya

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Wata kyakyawar budurwa ta zama mai takaba, kwanaki 12 bayan da suka yi aure da rabin ranta kuma masoyinta.

A yayin da ba a gano dalilin mutuwarsa ba kuma babu wanda ya bayyana, wasu bayanai kan ma'auratan sun bayyana a TikTok inda @glorycutex3 ta bayyana a bidiyo.

Ango ya rasu
Ango ya rasu bayan kwana 12 da aure, bidiyon aurensu da kyakyawar amaryarsa ya taɓa zukata. Hoto daga TikTok/@glorycutex3
Asali: UGC

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

A bidiyon, an bayyana cewa ma'auratan sun yi auren gargajiya a ranar 26 ga watan Mayu kuma daga bisani bayan kwanaki biyu suka yi na coci.

Wani gajeren bidiyon kyawawan ma'auratan a cikin shigar auren cocinsu yayin da suke cikin mota, tare da wani bidiyon amaryar na rike da amsa-kuwwa a taron ya bayyana.

Amma a ranar 9 ga watan Yunin, kwanaki 12 bayan auren cocinsu, angon yace ga garinku.

Sama da mutum 7.2 miliyan ne suka kalla bidiyon a yayin rubuta wannan rahoton yayin da ake ta kwarara sakonnin ta'aziyya ga kyakyawar amaryar kan wannan rashin da tayi mai girma.

Kalla bidiyon:

'Yan Najeriya sun yi mata ta'aziyya

Charitydauda847: "Yesu! Ina mishi fatan gafara. Ubangiji ya taimakemu kada mu taba fuskantar irin wannan."
Zimelfashion: "Wannan abun akwai kunar rai ga matar da iyalansa. Abun ya taba min zuciya. Ina fatan Ubangiji ya basu hakuri. Akwai sa ran haduwa a kiyama, zaku sake haduwa."

Joa Sharon Adokorach: "Wannan shekarar gani nan dai kawai bayan na rasa mahaifina a watan Yuni. Har yanzu ina kokarin karbar kaddaran ne amma abun babu sauki. Ubangiji ya gafarta maka babban aboki."

Cike da tashin hankali, matashi ya sanar da mutuwar budurwar da zai aura nan da sati 2

A wani labari na daban, rashin masoyi babban ibtila'i ne da kan fadawa 'dan Adam, sau da yawa a kan dade ana jinyar zuciya idan ta rasa abinda take so balle a ce mutuwa ce ta gifta.

Wani matashi mai suna Safiyanu Abubakar ya wallafa katin bikinsa wanda za a yi a ranar 12 ga watan Augutan 2022 da masoyiyarsa Rukaiya Ibrahim Salihu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel