Magajin Abba Kyari, DSP Disu ya je Amurka, Ya yi Wa Kasarsa Abin Alfahari
- DCP Tunji Disu wanda shi ne shugaban dakarun IRT na ‘yan sanda ya yi abin alfahari
- A ranar karshe na watan Yulin 2022, Tunji Disu ya samu nasara a gasar Judo da aka yi
- ‘Dan sandan ne ya zo na biyu a gasar shekarar nan wanda aka shirya a kasar Amurka
ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit
San Francisco - Shugaban rundunar IRT na ‘yan sandan Najeriya, DCP Tunji Disu ya nuna cewa bayan aikin kwalawa, akwai kuma inda ya kware.
Legit.ng Hausa ta fahimci DCP Tunji Disu ne ya zo na biyu a gasar damben Judo wanda aka shirya a birnin San Fransisco da ke kasar Amurka.
Jami’in ‘dan sandan ya tashi da Veteran Judo fighter Silver medal, ma’ana wanda ya lashe kyautar zama na biyu a gasar Judo na manya na 2022.
Wannan ne karo na 33 da aka shirya gasar Judo tsakanin kasashen Duniya a Amurka.
Joe Igbokwe ya yi masa barka
Joe Igbokwe ya wallafa hotunan Disu dauke da kyautar da ya samu a gasar. Igbokwe ya daura wadannan hotuna ne a shafinsa na Facebook.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
‘Dan siyasar kuma Hadimin gwamnan Legas ya taya ‘dan sandan murnar nasarar da ya samu. Sauran mutanen Facebook sun yi masa barka.
A wani hoton za a iya ganin DSP Disu rike da tutar Najeriya yana alfahari, a gefe za a ga ya rataya kyautar azurfar da ya samu a jikin wuyansa.
An shirya gasar bana daga ranar Alhamis 28 ga watan Yuli 2022 zuwa ranar Lahadi wanda ya kama 31 ga watan Agustan wannan shekarar.
Babban jami’in tsaron ya wallafa bidiyonsa a Twitter bayan ya samu nasara, aka ga wani tsohon zakaran Duniya yana mai taya shi farin ciki.
Baya ga haka an ga wasu bidiyoyin ‘dan sandan a dandalin Twitter yayin da yake dambatawa da abokan gabarsa a fili a makon da ya gabata.
Gwarzo Magajin Kyari
Shi dai Disu Olatunji Rilwan mataimakin kwamishinan ‘yan sanda ne wanda ya fara aikin damara a 1992, shi ne wanda ya canji Abba Kyari a IRT.
‘Dan sandan mai shekara 56 ya rike jagorancin rundunar RRS a Legas da bataliyar AU kafin yanzu. A watan Mayun 2026 ne zai yi ritaya daga aiki.
Tobi Amusan
A watan da ya gabata ne aka tashi da labarin farin cikin nasarar da Tobi Amusan ta samu a gasar tseren Duniya wanda aka yi a Oregon, Amurka.
Amusan wanda ‘Yar Najeriya ce ta samu gwal, ta kafa tarihi a wasannin Athletics Championships 2022, tayi tseren mita 100 a cikin dakika 12.12.
Asali: Legit.ng