Matashi Ya Shirya Angwancewa Da Kanwar Marigayiyar Budurwarsa Bayan Mako 1 Da Mutuwarta

Matashi Ya Shirya Angwancewa Da Kanwar Marigayiyar Budurwarsa Bayan Mako 1 Da Mutuwarta

  • A makon jiya ne labarin mutuwar wata budurwa mai suna Rukayya Ibrahim Kani wacce ake gab da aurenta ya karade shafukan sadarwa
  • Ba a fasa ba za a daurin auren a ranar 12 ga watan Agusta, sai dai da kanwarta Fatima Ibrahim Kani za a kulla shi
  • Babban wan marigayiyar ne ya sanar da sabon sauyin da aka samu a shafinsa na Facebook

Bauchi - Wani matashi dan Najeriya mai suna Sufiyanu Abubakar Salihu na shirin angwancewa da Fatima Ibrahim Kani, kanwar budurwarsa da ta rasu.

Tun farko dai an shirya yin auren Sufiyanu da Rukayya Ibrahim Kani a ranar 12 ga watan Agusta a jihar Bauchi amma sai Allah ya yi mata rasuwa a ranar Laraba, 27 ga watan Yuli.

Sufiyanu da kansa ya je shafin Twitter a ranar 28 ga watan Yuli inda ya sanar da rasuwar Rukaiya.

Kara karanta wannan

Da dumi-dumi: ‘Yan bindiga sun harbi shugaban 'yan sanda, sun kashe jami'in kariyarsa

Shirin Aure
Bayan Rasuwarta Ana Saura Kwana 15 Aurensu, Matashi Zai Auri Kanwar Budurwarsa A Ranar Da Aka Saka Masu Hoto: Aliyu Ibrahim Kani (SirLambo)
Asali: Facebook

Hakazalika, Fatima ta nuna bakin cikin rashin yar’uwar tata a shafinta na soshiyal midiya har ta nemi a taya yar’uwar tata da addu’a.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

“Tabbass, rayuwa mai karewa ne kuma mutuwa dole ce. Na sake rasa ‘yar’uwata Ruqayya Ibrahim Kani (Aunty Ummi), an saka ranar aurenta nan da makonni biyu masu zuwa amma ta tafi har abada. Ya Allah kagafarta mata kamata rahama kasa in tamu tazo mucika da imani. Dan Allah ku taya yar’uwata da addu’a.”

Babban yayansu, Aliyu Ibrahim Kani, ya je shafinsa na Facebook a ranar Laraba, 3 ga watan Agusta, inda ya sanar da cewar za a daura auren a wannan rana tsakanin Sufiyanu da Fatima.

Ya kuma wallafa sabon katin gayyatar auren inda sunan Fatima ya maye gurbin na Rukaiyya.

“Rayuwa na cike da darusa. Katin gayyatar daurin auren yar’uwata Fatima Ibrahim Kani Zara.

Kara karanta wannan

Bidiyon Kashim Shettima Yayin da Yake Sanyawa Diyarsa Fatima Albarka , Ya Yi Mata Kyautar Kudi Da Makulin Mota

“Da aka tunkare ni da batun sake kulla auren, sai da na dade kafin na yarda amma ba za mu ki yarda da cewar dole a ci gaba da rayuwa. Ina yiwa yar’uwata marigayiya addu’a Aunty ummi Allah ya jikanta Allah ya Mata rahama , Allah ya sanya alkhairi a cikin wanann aure da za ayi da zara'u. kuma kuna iya tunani son ranku amma addu’a shine abun da muke bukata a yanzu.
“Marigayiya Rukayya Ibrahim Kani ta mallaki digiri a bangaren lafiya haka ma Zara daga jami’ar jihar Bauchi. Ita ke biwa marigayiya Aunty Ummi uwa daya uba daya. Komai nasu iri daya ne. Gashi zai sake faruwa. Wannan darasi ne kuma duk muna godiya ga iyayenmu da kuma Malam Sufiyan da Yar’uwa Zara. Allah ubangiji ya kaimu lokaci Allah ya sanya alkhairi. Allah ya jikan Aunty ummi.”

Matar Aure Tayi Hayar Macen Da Za Ta Dinga Gamsar Da Mijinta, Ta Saka Mata Albashin N145K Duk Wata

Kara karanta wannan

Shagalin Biki Na Manya: Hotuna Da Bidiyo Sun Bayyana Daga ‘Kunshin’ Fatima Shettima

A wani labarin, wata mata tayi hayar wacce za ta taimaka mata wajen biyawa mijinta bukata ta bangaren kwanciyar aure bayan ta tallata aikin a yanar gizo.

Matar mai shekaru is 44 mai suna Patheema daga kasar Thailand, ta je shafin Tiktok ta tallata aikin mai ban al’ajabi.

Ta yi bayani yayin tallata aikin cewa tana son daukarwa mijinta hayar sa-‘daka domin ta yarda cewa bata gamsar da shi a gado, shafin LIB ya rahoto.

Asali: Legit.ng

Online view pixel