Muna Bukatar Shirin Da Zai Daura Mu Sama Da Yan Ta’adda – Osinbajo Ya Fadawa Sojoji
- Yemi Osinbajo ya ce akwai bukatar gwamnatin Najeriya ta yi shirin da zai sanya su kan gaba da tunanin yan ta’adda
- Mataimakin shugaban kasa ya yi kira da sojoji da masu ruwa da tsaki da kara kaimi wajen kirkiran makamai a cikin gida
- Shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa, Farfesa Ibrahim Gambari yana cikin wadada suka halarci Taron Da Osinbajo ya jagoranta
Abuja - Mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo ya ce akwai bukatar gwamnatin Najeriya ta dauki matakin da zai sanya tunanin su gaba da ‘yan ta’adda da ke barna a fadin kasar. Rahoton Channels TV
Ya ce kalubalen tsaro da kasar ke fuskanta a halin yanzu da barazanar da ke kunno kai, yana bukatar sojoji da sauran masu ruwa da tsaki su kasance cikin shiri tare da kara kaimi wajen kirkiran makamai a cikin gida.
Wannan shi ne daya daga cikin muhimman abubuwan da Osinbajo ya mayar da martani akai a wani taron tattaunawa mai zurfi da ya halarta a Kwalejin Tsaro na kasa mai Taken "Tsarin Tsaro na Kasa a yammacin ranar Laraba.
Osinbajo yace Idan aka yi la’akari da irin kalubalen tsaro da kasar ke fuskanta, ya zama dole mu kasance da tsare-tsare da matakai da zai samu kan gaban da yanta’ada
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
An nakalto mataimakin shugaban kasar yana fadar haka a wata sanarwa da kakakinsa Laolu Akande ya fitar ranar Alhamis.
Sauran jami’an da suka halarci taron sun hada da shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa, Farfesa Ibrahim Gambari; Babban Hafsan Sojin Ruwa, Vice Admiral Awwal Gambo; Kwamandan Kwalejin Tsaro ta kasa Rear Adm. Murtala Bashir, da kuma wakilin Sufeto Janar na 'yan sanda da sauran manyan jami'an kwalejin
Bayan Umarinin Buhari, Sojoji Za Su Gudanar Da Wani Atisaye Mai Taken ‘Operation Babu
A wani labari kuma, Abuja - Hafsoshin jami’an tsaro sun fara aiwatar da umarnin shugaban kasa Muhammadu Buhari na dakatar da hare-hare da kashe-kashen da ‘yan ta’adda ke yi nan take. Rahoton LEADERSHIP
A jiya ne hafsoshin Rundunar sojoji suka kaddamar da wani Atisaye mai Taken “Operation Show No Mercy wato Nuna ‘Yan Ta’adda rashin Tausayi”.
Asali: Legit.ng