Bayan Umarinin Buhari, Sojoji Za Su Gudanar Da Wani Atisaye Mai Taken ‘Operation Babu Tausayi'

Bayan Umarinin Buhari, Sojoji Za Su Gudanar Da Wani Atisaye Mai Taken ‘Operation Babu Tausayi'

  • Hafsoshin jami’an tsaro sun fara aiwatar da umarnin shugaban kasa Muhammadu Buhari na dakile hare-hare da kashe-kashen da ‘yan ta’adda ke yi
  • Rundunar sojojin Najeriya ta kaddamar da sabon Atisaye mai Taken “Operation Show No Marcy wato Atisayen Nuna Wa ‘Yan Ta’adda rashin Tausayi'
  • A watan da ya gabata wasu yan bindiga suka kai wa jami'an sojoji kantar bauna a cikin birinin Abuja

Abuja - Hafsoshin jami’an tsaro sun fara aiwatar da umarnin shugaban kasa Muhammadu Buhari na dakatar da hare-hare da kashe-kashen da ‘yan ta’adda ke yi nan take. Rahoton LEADERSHIP

A jiya ne hafsoshin Rundunar sojoji suka kaddamar da wani Atisaye mai Taken “Operation Show No Mercy wato Nuna ‘Yan Ta’adda rashin Tausayi”.

Shugaban Rundunar Sojan Sama (CAS), Air Marshal Oladayo Amao, ya bayyana haka a wata jawabi da ya fitar a jiya a birnin Abuja.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Sojoji Sun Kai Samame Maɓoyar Yan Ta'adda, Sun Halaka Dandazon Su A Jihar Arewa

Armyn
Bayan Umarinin Buhari, Sojoji Za Su Gudanar Da Wani Atisaye Mai Taken ‘Babu Jinkai FOTO PUNCH
Asali: UGC

Ya umurci kwamandojin rundunar sojojin saman Najeriya (NAF) da ke aiki a sassa daban-daban na kasar nan da su ‘nuna rashin tausayi’ tare da yin amfani da karfin wuta a kan ‘yan ta’adda da ke barazana ga tsaro ga al’ummar kasar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A watan da ya gabata ne Legit.NG Ta rawaito labarin yadda yan bindiga suka kai wa dakarun sojojin kare shugaban kasa na Brigades harin kantar Bauna a brinin Abuja inda suka kashe sojoji shida da raunata wasu.

Yanke Wa Mutane Lantarki Ba Tare Da Ba Su Gargadin Kwana 10 Ba Ya Saba Wa Doka – FCCPC

A wani labari kuma, Jihar Kuros Ribas - Yanke wutar Lantarkin mutanen da ba su biya kudi ba ba tare da ba su gargadin kwana goma daga kamfanonin rarraba wuta na DISCO ya sabawa doka inji hukumar Hukumar Kula da Gasa da Kare Hakkin Masu Sayen Kaya ta Kasa (FCCPC).Rahoton Aminiya. DailyTrust

Babatunde Irukera, Mataimakin Shugaban Hukumar FCCPC, ya bayyana haka ne a wani shirin warware korafin masu amfani da wutar lantarki da hukumar FCCPC ta shirya a jihar Kuros Ribas.

Asali: Legit.ng

Online view pixel