Matar Aure Tayi Hayar Macen Da Za Ta Dinga Gamsar Da Mijinta, Ta Saka Mata Albashin N145K Duk Wata

Matar Aure Tayi Hayar Macen Da Za Ta Dinga Gamsar Da Mijinta, Ta Saka Mata Albashin N145K Duk Wata

  • Wata matar aure tayi abun mamaki na daukowa mijinta hayar macen da za ta dunga gyara masa shimfida
  • Patheema ta ce ba za ta iya gamsar da mijin nata ba a bangaren kwanciyar aure don haka ta samo wacce za ta taimaka mata
  • Ta samu wacce ta nuna sha'awar wannan aiki bayan ta tallata shi a yanar gizo, kuma za a dunga biyanta albashi duk wata

Wata mata tayi hayar wacce za ta taimaka mata wajen biyawa mijinta bukata ta bangaren kwanciyar aure bayan ta tallata aikin a yanar gizo.

Matar mai shekaru is 44 mai suna Patheema daga kasar Thailand, ta je shafin Tiktok ta tallata aikin mai ban al’ajabi.

Ta yi bayani yayin tallata aikin cewa tana son daukarwa mijinta hayar sa-‘daka domin ta yarda cewa bata gamsar da shi a gado, shafin LIB ya rahoto.

Kara karanta wannan

Jarumar Mata: Yadda Uwargida Ta Rungume Amaryar Mijinta A Wajen Dinan Aurensu, Bidiyon Ya Haddasa Cece-Kuce

Matar aure
Matar Aure Tayi Hayar Macen Da Za Ta Dinga Gamsar Da Mijinta, Ta Saka Mata Albashin N145K Duk Wata Hoto: LIB
Asali: UGC

Matar ta bayyana a bidiyon cewa:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

“Ina son daukarwa mijina hayar sa-‘daka guda uku.”

Ta kuma jaddada a bidiyon cewa dole matan su kasance tsakanin shekaru 30-35 kuma ya zamana sun kammala kwaleji ko suna da digiri.

Matar ta kuma bayyana cewa dole sa-’dakar ta kasance da takardar gwajin lafiya don tabbatar da basa dauke da cutar kanjamau.

Bidiyon tallan ya ci gaba da cewa:

“Za a biya ta akalla £340 (N145k a kudin Najeriya) duk wata, za a baku wajen kwana da abinci kyauta. Amma ya zama dole ku taimaka mun. Mutum biyu za su dunga taimakamun da aiki kan takardu a ofishina, sannan mutum daya za ta kula da mijina da yarana.”

Matar ta kuma ba wadanda za su nemi aikin tabbacin cewa ba za ta raina mai debewa mijin nata kewa ba.

Kara karanta wannan

Bidiyon Yadda Wata Amarya Da Mahaifinta Suka Fashe Da Kuka A Wajen Liyafar Bikinta

“Ina mai ba da tabbacin cewa fada ba zai shiga tsakaninki da ni ba. Zan bari mijina ya zabi da wacce yake so ya kwanta ko yake so tsaya da ita. Ba raba lokaci, zai iya zaba da kansa,” in ji ta.

Duk da abun al’ajabin da ke tattare da wannan aikin, ma’auratan sun samu wacce ke sha’awar aikin kuma sun karbeta hannu bibbiyu a gidansu.

An tattaro cewa Patheema ta bukaci wata kyakkyawar mata mai shekaru 33 da ta shigo cikin ahlinta a matsayin sa-‘dakar mijinta.

Ta kuma ce koda dai ba macen da mijinta ya yi tsammanin samu bane, ya yarda ta zama ‘karamar matarsa’, kuma Pattheema ta rufe daukar aikin.

Matar ta kasance aminiyar Pattheema kuma su dukka ukun sun ce suna shirin kula da junansu.

Budurwa Ta Gane Cewa Mijinta Gurgu Ne Bayan Aurensu, Da Kafafun 'Acuci' Ya Dinga Zuwa Tadi, Bidiyo

A gefe guda, labarin wasu masoya mai taba zukata ya bayyana a shafin soshiyal midiya, inda mijin ya boyewa amaryarsa cewa shi gurgu ne har bayan aurensu.

Kara karanta wannan

Biki ya yi biki: Bidiyon yadda amarya tayi jifa da gwagwaro da takalmi tana cashewa a bikinta

Mutumin da aka ambata da suna Jado da masoyiyarsa Bora sun shafe tsawon lokaci suna soyayya kafin suka yi aure.

A tsawon lokacin da suka shafe suna soyayya, Jado ya boyewa Bora cewa bai da kafafuwa saboda tsoron kada ta fasa aurensa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel