2023: Atiku ya nada Dino Melaye da Daniel Bwala mukamai a tawagar kamfen dinsa

2023: Atiku ya nada Dino Melaye da Daniel Bwala mukamai a tawagar kamfen dinsa

  • Dan takarar shugaban kasa a jam'iyyar PDP ya nada wasu jiga-jigan siyasar Najeriya kan wasu mukamai
  • Dino Melaye da Daniel Bwala su ne masu magana da yawun tawagar yakin neman zaben Atiku Abubakar
  • Jam'iyyun siyasa na ci gaba da nade-nade a shirin kawo kujerar shugaban kasa a zaben 2023 mai zuwa

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Najeriya - Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP Atiku Abubakar ya bayyana Sanata Dino Melaye da kuma Dokta Daniel Bwala a matsayin masu magana da yawun tawagar yakin neman zabensa.

Nadin nasu na kunshe ne cikin wata ‘yar gajeruwar sanarwa ta hannun mai baiwa Atiku shawara kan harkokin yada labarai, Paul Ibe, inda ya ce nadin na su ya fara aiki nan take, Channels Tv ta ruwaito.

Malaye da Bwala sun samu mukami a tawagar kamfen din Atiku
2023: Atiku ya nada Dino Melaye, Daniel Bwala a matsayin kakakin yakin neman zaben | Hoto: channelstv.com
Asali: UGC

A cewar Ibe:

Kara karanta wannan

Rikicin siyasa: Tsigaggen mataimakin gwamnan PDP ya ja zuga, masoyansa sun koma APC

“Melaye dan siyasa ne kuma dan majalisar dattawa ta 8 da ke wakiltar mazabar Kogi ta Yamma. Ya fito daga Ayetoro Gbede da ke karamar hukumar Ijumu a jihar Kogi.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

“Bwala, a daya bangaren, kwararre ne a fannin shari’a, dan siyasa, kuma mai sharhi kan al’amuran jama’a. Ya fito ne daga jihar Adamawa.”

Hukumar zabe ta INEC ta sanya ranar 28 ga Satumba, 2022 a matsayin ranar da za a buga gangar siyasa na neman zaben shugaban kasa da na ‘yan majalisun tarayya, yayin da na gwamnoni da na majalisun jihohi za a buga gangarsu a ranar 12 ga Oktoba, 2022, inji TheCable.

Jam'iyyun siyasa a Najeriya na ci gaba da shirye-shiryen fuskantar zaben 2023 da za a yi nan da watanni kadan.

Rashin Tsaro: Za Mu Yi Duk Mai Yiwuwa Don Ganin an Gudanar da Zaben 2023, In Ji FG

Kara karanta wannan

Wata sabuwa: Sakateriyar PDP ta dagule, ana ta kira ga tsige shugaban jam'iyya

A wani labarin, gwamnatin tarayya ta ce za ta yi duk mai yiwuwa domin ganin an gudanar da babban zaben 2023 duk da kalubalen tsaro da kasar ke fuskanta.

Lai Mohammed, ministan yada labarai da al'adu ne ya bayyana hakan a ranar Laraba yayin da yake jawabi ga manema labarai bayan taron majalisar zartarwa ta tarayya (FEC), TheCable ta ruwaito.

A cewarsa, duk da damuwar da ake da ita kan kalubalen tsaro, gwamnatin tarayya na ci gaba da jajircewa wajen inganta rayuwar ‘yan Najeriya ta hanyar samar da tsaro da inganta rayuwar jama’a abin da ta fifita kan komai, Daily Sun ta ruwaito.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.