Matakai 10 da Sanatoci Za Su Bi Kafin Su Iya Tunbuke Shugaba Buhari a Majalisa
- A ‘yan kwanakin nan ‘Yan majalisa sun fara maganar tunbuke Muhammadu Buhari daga mulki
- Akwai wasu matakai da kundin tsarin mulki ya yi tanadi kafin a iya sauke shugaban Najeriyan
- Da zarar an yi nasarar sauke shugaban kasa, babu wanda ya isa ya dawo da shi kan kujerar mulki
Wannan rahoto ya tattaro maku matakan da ke gaban ‘yan majalisa kamar yadda sashe na 143 na kundin tsarin mulkin 1999 ya yi tanadi:
Ya abin yake?
Mataki na 1: A fito da zargin da ake yi
Da farko za a samu akalla kashi biyu cikin uku na ‘yan majalisa sun rubuta takarda zuwa ga shugaban majalisa, suna bayanin zargin laifin da ake yi wa shugaban kasa.
Mataki na 2: A sanar da Shugaban kasa
Bayan nan sai shugaban majalisar dattawa ya sanar da shugaban kasa laifin da ake tuhumarsa da aikatawa. Za a aika takarda bayan kwanaki bakwai da fara bincike.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Mataki na 3: Martanin Shugaban kasa
Daga nan kuma sai shugaban kasar ya maida martani ga majalisa. A nan mai mulki zai wanke kan shi a wajen ‘yan majalisar tarayya daga zargin da aka jefe sa da shi.
Mataki na 4: Bincike a kan zargin
Bayan kwanaki 14 sai ‘yan majalisa su tattauna kan maganar fara binciken zargin da aka yi wa shugaban Najeriyan. Za ayi wannan ba tare da la’akari da martaninsa ba.
Mataki na 5: Bayan an yi muhawara
Da zarar an gagara samun amincewar kashi biyu cikin uku na ‘yan majalisa, za ayi watsi da maganar. Idan akasin haka ya tabbata, za a nemi tunbuke shugaban kasar.
Mataki na 6: Shugaban kasa zai kare kan shi
A nan za a bukaci shugaban kasa ko Lauyansa ya wanke shi a gaban kwamitin mutum bakwai da Alkalin Alkalai zai kafa wanda zai kunshi mutanen kwarai.
Mataki na 7: Aikin kwamitin bincike
Kwamitin binciken da shugaban Alkalai na kasa zai kafa zai yi watanni uku yana aiki. Daga nan zai gabatar da rahoton aikin da ya gudanar a gaban majalisar tarayya.
Mataki na 8: Idan zargin ba gaskiya ba ne
Muddin kwamitin ya gano zargin da ake yi wa shugaban kasar ba gaskiya ba ne, ya zama dole Sanatoci suyi watsi da yunkurin, babu maganar a sauke shugaban kasar.
Mataki na 9: Idan zargin gaskiya ne
Idan aka tabbatar da shugaban kasa ya aikata laifin da majalisar tarayya take zarginsa, za a ba majalisa kwanaki 14 domin su duba rahoton da kwamiti ya gabatar.
Mataki na 10: Amfani da rahoton
Idan an zo nan, Sanatoci za su karbi rahoton binciken, su amince da shi idan an samu rinjaye. An sauke shugaban kasa daga ranar da aka yi wannan, magana ta kare.
Dole ayi hattara - Majalisa
Dazu aka ji Hon. Ben Kalu yana cewa kafin 'Yan Majalisa su fara maganar sauke Shugaban Najeriya har zuwa lokacin da za a kammala, za a dauki lokaci.
Mai magana da yawun bakin ‘Yan Majalisar Wakilan kasar yace dole sai an yi taka-tsan-tsan sosai da maganar tunbuke Muhammadu Buhari daga kan mulki.
Asali: Legit.ng