Obasanjo ya cire Buhari daga sunayen shugabannin Afrika dake kawo chanji a shugabanci
- Tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo, ya yaba ma shugaban kasa Allassane Ouatarra na d’Ivoire kan mayar da hankali wajen gyara a wannan kasar
- Ya yaba ma shugaban kasar Côte d’Ivoire kan matakin gaggawa day a dauka don magance kasar bayan rikici da akayi a zaben sa a shekarar 2011
- Obasanjo ya yi ikirarin cewa lokaci bai yi bad a zai bayyana wanda zai marawa baya a zaben shugabancin kasa na 2019
Tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo ya cire shugaban kasa Muhammadu Buhari daga sunayen shugabannin Afrika da yake ganin sun yi nasara wajen habbataka tattalin arziki da kuma bin tsari da bukatan wannan karni da muke ciki.
A lokacin da yake jawabi akan shugabanci a jami’ar Oxford a ranar Litin, 8 ga watan Janairu, a makarantar gwamnatin Blavatnik, Obasanjo ya yabi shugabannin Afrika guda uku kan irin yadda suke gudanar da shugabancinsu, jaridar Premium Times ta ruwaito.
Musamman tsohon shugaban kasar ya yaba ma shugaban kasa Allassane Ouatarra na Côte d’Ivoire kan mayar da hanlkali da yayi wajen gyara abubuwa a kasar.
Obasanjo ya ce Ouatarra matakin gaggawa wajen gyara kasar bayan rikici day a afku lokacin zaben sa a 2011.
KU KARANTA KUMA: Gwamnatin tarayya ta nada Attahiru Jega da sauransu domin su sake duba ga tsarin jami’an Najeriya
Ya kuma ambaci Rawanda da Ethiopia a matsayin sauran kasashe dake kokari tare da Côte d’Ivoire.
Amma dai tsohon shugaban kasar bai ambaci Buhari, wanda ya mara ma baya a lokacin zaben 2015.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng