Mijina Raggo Ne, Ya Boye A Bandaki Lokacin Da Yan Fashi Suka Shigo Gidanmu, Mata Mai Neman Saki
- Wata mata mai suna Asiata Oladejo ta yi karar mijinta Abidemi a kotu kan zarginsa da yin watsi da ita da yaranta a lokacin da yan fashi suka kawo hari gidansu
- Asiata, wacce yar kasuwa ce ta fada wa kotu cewa Abidemi ya shige bandaki ya boye ya bar da yara a gaban yan fashi kuma bai fito ba har sai da yan fashin suka tafi
- Abidemi ya amsa wa kotu cewa tabbas ya boye a bandakin amma ya kuma ce yana ta kokarin bata hakuri domin ta daure su cigaba da zama tare amma ta ki amincewa
ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit
Oyo - Wata yar kasuwa, Asiata Oladejo, ta roki kotun gargajiya da ke zamanta a Mapo, Ibadan Jihar Oyo, ta warware aurenta saboda mijinta, Abidemi, ya tsere ya bar ta hannun yan fashi a lokacin da suka kawo musu hari.
Asiata ta bayyana hakan ne a ranar Laraba a karar da ya shigar na neman saki kamar yadda Daily Trust ta rahoto.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Ta fada wa kotun, "Har yanzu ban gama watsakewa ba daga firgicin da na shiga lokacin da gungun barayi suka afko mana gida.
"Shi (mijina) ya boye a bandaki; ya bar ni ina haki a gaban yan fashin wadanda suka tada wa kowa a gidan hankali.
"Lokacin da barayin suka shigo gidan misalin karfe 1 na dare, miji na bai tsaya ya kare ni da yara ba.
"Ya boye a bandaki. Sai da barayin suka tafi ya fito kuma yana son mu cigaba da zama a gida daya."
Ta ce ta roke shi ya kama wani gidan hayan daban, amma ya ki, kuma tana zarginsa da bin wasu mata a waje.
Martanin Abidemi
Abidemi, wanda tela ne, ya shaidawa kotun cewa matarsa ta cika fitina.
Ya ce, "Tana zuwa shago na ba tare da ta sanar da ni ba ta gallaza min.
"Gaskiya ne na boye a bandaki lokacin da yan fashi suka kawo hari gidan mu. Na yi kokarin ta dawo gida amma bai yiwa ba saboda tana tsoro."
Ya roki kotun ta bashi ikon rike yaransu uku domin ya kasance mahaifi na gari gare su.
Hukuncin da kotu ta yanke
A hukuncinta, Shugaban kotun, Mrs S.M. Akintayo ta umurci Asiata ta dena yin barazana ga rayuwar Abidemi ko muzguna masa.
Amma ta bawa Asiata ikon rike yaran uku tana mai cewa ita ce ta fi dacewa ta kula da su.
Ta kara da cewa "Mai karar da wanda aka yi kara za su rika kula da walwala da ilimin yaran.
"Bugu da kari, Abidemi zai rika biyan N20,000 duk wata don abinci da kula da yaran.
"Dole dukkan ku ku zauna lafiya."
Amma, ta ce babu auren da za a warware tsakaninsu tunda dama ba su yi aure ba karkashin dokokin Najeriya.
Zamfara: Kotun Musulunci Ta Raba Auren Shekara 23 Tsakanin Wani Mutum Da Jikarsa
A wani rahoton, wata babban kotun shari'a da ke Tsafe, a karamar hukumar Tsafe na Jihar Zamfara a ranar Talata ta raba auren shekaru 23 tsakanin wani mutum Musa Tsafe da jikarsa, Wasila.
Yayin yanke hukuncin, alkalin kotun, Malam Bashir Mahe, ya raba auren bayan ya saurari bangarorin biyu wato masu kare da wadanda aka yi kara.
Alkalin ya ce aure tsakanin mata da mijin ya saba wa sura ta 3 aya ta 23, shafi da shafi na 79 da 77 na ihkamil Ihkami.
Asali: Legit.ng