Buhari Zai Raba Tallafin N38bn ga ‘Yan Najeriya Miliyan 1.9, ga Jihohin da Za Su Samu

Buhari Zai Raba Tallafin N38bn ga ‘Yan Najeriya Miliyan 1.9, ga Jihohin da Za Su Samu

  • Gwamnatin Najeriya na shirin ba da tallafin N38bn ga ‘yan Najeriya kimanin Naira miliyan 1.9 a karkashin shirinta na ba da tallafi
  • A cewar ma'aikatar jin kai da walwala, shirin na da nufin taimakawa 'yan Najeriya miliyan 100 don tsamo su daga kangin talauci cikin shekaru 10
  • Ma’aikatar ta ce tuni ta fara bayar da kudaden tallafin a babban birnin tarayya Abuja bayan kaddamar dashi

Gwamnatin Buhari ta shirya cire 'yan Najeriya akalla miliyan biyu daga kangin talauci ta hanyar raba musu N20,000 kowane a karkashin shirin tallafawa marasa galihu.

Rahoton da Legit.ng Hausa ta samo ya gano cewa, shirin na zuwa ne a karkashin ma'aikatar jin kai, kuma tuni an tattara bayanan bankin wadanda za su ci gajiyar shirin.

Kara karanta wannan

Ba zai yiwu ba: Pantami ya tubure, ya ce ba zai bari a kara harajin katin waya da data ba

Yadda Buhari ya shirya rabawa 'yan Najeriya kudade
Buhari zai raba tallafin N38bn ga ‘yan Najeriya miliyan 1.9, ga jihohin da za su samu | Hoto: premiumtimesng.com
Asali: UGC

Shirin fitar da ‘yan Najeriya miliyan 100 daga kangin talauci

Sadiya Umar Faruk, minstan ma'aikatar ta jin kai tuni aka ce ta fara raba kudaden ga mazauna babban birnin tarayya Abuja, kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Hakazalika, ministar ta yiwa tsarin baya na Cash Grant da ake raba rabawa mata a karkara zuwa Grant for Vulnerable Groups domin karfafawa marasa galihu.

Rahoton ya ce, Sadiya ta ambaci shekarar da aka kaddamar da shirin, inda tae gwamnatn Buhari ce ta kawo a 2020, shekarar da aka dandana annobar Korona.

Da take bayani game da shirin da gwamnatin ta ware N38bn domin kashewa jihohi 36 na kasar nan, ministar ta ce:

“An tsara shi ne don bayar da tallafin sau daya ga marasa galihu da mata masu rauni a yankunan karkara da kewayen kasar nan. Ana raba tallafin kudi ne na Naira 20,000 ga marasa galihu mata da matasa a fadin jihohi 36 na tarayya da kuma babban birnin tarayya.

Kara karanta wannan

An samu ci gaba: Minista Pantami ya haramta shigo da layukan waya daga kasashen waje

“Manufarmu a babban birnin tarayya Abuja shine mu raba tallafin ga sama da mutane 2,900 da suka ci gajiyar tallafin a fadin kananan hukumomin shida.
"Daidai da shirin shugaban kasa Muhammadu Buhari na walwalar jama'a, 70% cikin 100% na wadanda za su ci gajiyar tallafin mata ne yayin da sauran kashi%30 cikin 100% kuma maza ne.”

A ina ta samo: Gwamnatin Buhari ta kame malamar makaranta da laifin mallakar N500m

A wani labarin, a ranar Alhamis, 28 ga watan Yuli ne hukumar yaki da cin hanci da rashawa mai zaman kanta ta ICPC ta bayyana cewa ta gano jimillar Naira miliyan 540 a asusun wata malamar makarantar firamare na gwamnati mai karbar albashin N76,000.

Jaridar Premium Times ta ruwaito cewa babbar kotun tarayya da ke zamanta a Abuja ta kuma bayar da umarnin a kwace Naira miliyan 120 na malamar, Roseline Egbuha da ke koyarwa a makarantar firamare ta Ozala, Abagana ta jihar Anambra.

Kara karanta wannan

Kano Ta Amince Da Yiwa Daliban Jihar Karin Tallafin Alawus Da Kashi 50

Wata sanarwa da mai magana da yawun hukumar, Azuka Ogugua ya fitar ta ce kotun ta mai shari’a D.U Okorowo ta kuma bayar da umarnin a kwace motocin da aka gano Egbuha ta mallaka da wasu kayayyakinta da ake zargi na haramun ne.

Asali: Legit.ng

Online view pixel