Da Dumi-Dumi: An Kona Gidan Jigon Jam'iyyar APC, Alhaji Abubakar Usman

Da Dumi-Dumi: An Kona Gidan Jigon Jam'iyyar APC, Alhaji Abubakar Usman

  • Wasu mutane da ba a san ko su wanene ba sun cinna wuta a gidan jigon jam'iyyar APC a Jihar Benue, Alhaji Abubakar Usman aka Young Alhaji
  • Alhaji Usman ya tabbatar da afkuwar lamarin inda ya ce wutan ta kona dakin mai gadi a gidansa da ke Otukpo kuma sh da ma'aikatan suka kashe wutan
  • Jigon na APCn ya ce ya sanar da DSS da yan sanda kuma duk da baya zargin kowa yana kyautata zaton wadanda suka aikata abin suna da kusanci da wasu yan APC a mazabarsa

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Benue - Rikicin jam'iyyar APC a Jihar Benue ya dauki sabon salo a yayin da wasu bata gari, a safiyar ranar Laraba suka cinna wuta a gidan jigon jam'iyyar APC, Alhaji Abubakar Usman wanda aka fi sani da Young Alhaji a Otukpo a Jihar Benue.

Kara karanta wannan

Wata sabuwa: Sakateriyar PDP ta dagule, ana ta kira ga tsige shugaban jam'iyya

The Punch ta rahoto cewa wasu bata gari da ba a sani bane, misalin karfe uku na dare suka cinnawa gidan da ke GRA a Otukpo wuta.

Wuta a Gidan Young Alhaji.
An Kona Gidan Jigon Jam'iyyar APC, Alhaji Abubakar Usman. Hoto: @MobilePunch.
Asali: Twitter

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Wutan ta cinye gaban gidan inda dakin mai gida da wasu gidaje suke.

Alhaji Abubakar, wanda ya taba yin sanata sai daya a Benue South, kwanaki kadan da suka wuce ya nuna akwatin gawa da littafin ta'aziyya don zolayar jam'iyyar APC a gaban gidansa.

Wasu yan jam'iyyar sun yi wa hakan fassara da cewa jam'iyyar APC ta mutu a jihar.

Abubakar da wasu yan APC a jihar sun yi baje kolin akwatin gawar ne don nuna rashin jin dadinsu bisa zabin dan takarar mataimakin gwamna a jihar.

Abubakar ya tabbatar da afkuwar gobarar

Da aka tuntube shi a wayar tarho, Alhaji Abubakar, wanda ya tabbatar da gobarar ya ce shi da kansa ya ajiye akwatin gawar a kofar gidansa don sanar da shugabannin jam'iyyar cewa akwai matsala a jam'iyyar a yankinsu.

Kara karanta wannan

Elrufai Ya Ce APC ta Riga Ta Nada Darakata Janar Na Kamfen Din Takarar Tinubu Da Shettima

Ya ce, "Eh, sun cinna wa gida na wuta a Otukpo. Wutan ya shafi dakin mai gadi."

Da aka masa tambaya ko menene dalilin da yasa ya saka akwatin gawa na zolaye a gaban gidansa, Abubakar ya ce:

" Na ajiye akwatin gawar ne don nuna cewa jam'iyyar mu ta APC ta kusa mutuwa kuma akwai bukatar a cece ta. Sako ne kawai.
"Yau ne rana na hudu da ajiye akwatin gawar a gaban gida na, ni ne na ajiye a nan. Na yi hakan don abin da ke faruwa a yankin mu a jam'iyyarmu. Na yi hakan ne don nuna cewa idan ba a dauki matakin gaggawa ba jam'iyyar za ta mutu.
"Rikicin saboda takarar mataimakin gwamna ne inda wasu mutane kamar John Ochoga, Simon Shango, da Tilley Gyado suke son a zabi Samuel Ode yayin da ni a matsayin jagoran jam'iyyar a yankin aka fada min kujerar ta tafi wurin Apa/Agatu."

Kara karanta wannan

Tsintsiya ta tsinke a Borno: Dan a mutun Tinubu ya sauya sheka zuwa jam'iyyar PDP

Jigon jam'iyyar wanda ya ce ba zai fita ba ya ce baya zargin kowa, "amma duk wanda ya aikata abin ba shi da nisa daga mamban jam'iyyarsu a yankinsu."
Ya kara da cewa, "sun kona gidan mai gadi na. Yan sanda da DSS sun sami. Ni da ma'aikata na muka kashe wutan."

Martanin yan sanda

An yi kokarin ji ta bakin mai magana da yawun yan sandan jihar, Catherine Anene, amma hakan bai yiwu ba domin bata dauki waya ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164