Da dumi-dumi: ‘Yan bindiga sun harbi AIG na 'yan sanda, sun kashe jami'in kariyarsa

Da dumi-dumi: ‘Yan bindiga sun harbi AIG na 'yan sanda, sun kashe jami'in kariyarsa

  • Yanzu muke samun labarin cewa, wasu 'yan bindiga sun farmaki AIG na 'yan sanda na shiyyar jihar Bauchi
  • An hallaka jami'in tsaro yayin da AIG din kuma aka harbe shi amma ya tsallake rijiya da baya, inji rahotanni
  • Hukumar 'yan sanda ba ta bayyana halin da yake ciki ba, amma ta ce yana raye kuma yana karbar kulawar asibiti

Jihar Kaduna- Wasu ‘yan ta’adda sun kai farmaki kan ayarin motocin mataimakin sufeto Janar na ‘yan sanda na shiyya ta 12 da hedikwatarsa da ke Bauchi, Audu Madaki, inda suka raunata shi tare da kashe daya daga cikin jami’an tsaronsa.

Ya zuwa lokacin tattara wannan rahoto, an gano cewa AIG din na kan hanyarsa ta zuwa Abuja daga Bauchi ne wasu da ake zargin ‘yan bindiga ne suka yi wa motarsa kwanton bauna.

Kara karanta wannan

Allah ya bada sa’a: Fitaccen Farfesa Yana Goyon Bayan Tsige Buhari da Gwamnoni

An farmaki AIG a Bauchi
Da dumi-dumi: ‘Yan bindiga sun farmaki AIG na'yan sanda, sun kashe jami'in kariyarsa | Hoto: channelstv.com
Asali: UGC

An ce lamarin ya faru ne a tsakanin Barde da Jagindi a jihar Kaduna a ranar Talata da misalin karfe 2:30 na rana, Punch ta ruwaito.

Wata majiya a hedikwatar shiyya ta 12 ta shaida cewa an harbi AIG Audu Madaki a yayin harin, yayin da aka harbe jami'in tsaronsa har lahira.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

An ce AIG din yana karbar magani a wani asibiti da ba a bayyana ba yayin da aka tsaurara matakan tsaro a kewayen shiyyar.

Wata majiyar kuma ta bayyana cewa an tura jami’an ‘yan sanda dauke da makamai zuwa yankin domin fatattakar ‘yan ta’addan tare da tsaftace dajin.

Yana raye, amma ya jikkata

Jaridar TheCable ta tuntubi Thomas Goni, mai magana da yawun ‘yan sandan shiyya ta 12, don jin ta bakinsa game da lamarin, ya ce har yanzu bai samu cikakken bayani kan harin ba.

Kara karanta wannan

Har yanzu akwai harsashi a ciki na: Bidiyon labarin fasinjan jirgin Abd-Kad a hannun 'yan bindiga

Amma ya yi karin haske da cewa:

"Har yanzu muna jiran cikakken bayani kan lamarin.
“Kun san hakan bai faru a yankinmu ba; Hakan ya faru ne a rundunar Kaduna don haka nake kan neman Kaduna don samun cikakkun bayanai daga wurinsu.

Rashin Tsaro: IGP Ya Umarci a Zagaye Babban Birnin Tarayya Abuja da Tulin Jami’an Tsaro

A wani yunkuri na kawar da fargabar mazauna Abuja dangane da barazanar tsaro da ake gani a baya-bayan nan, Sufeto Janar na ‘yan sandan Najeriya, IGP Usman Alkali Baba ya ba da umarnin tura karin jami’an ‘yan sanda masu yawan gaske zuwa birnin.

A cewar sanarwar da rundunar ta fitar, an dauki matakin ne domin karfafa tsaro da kare rayuka da dukiyoyin mazauna, muhimman kadarorin kasa da dai sauran ababe a zagayen birnin tarayya Abuja.

IGP ya ba da wannan umarni ne a yayin taron da rundunar ta gudanar a ofishinsa, yayin da yake samun cikakken bayani kan harkokin tsaro a kasar.

Kara karanta wannan

Bidiyo: Ana Tsaka Da Ruwan Sama, Tsoho Ya Rikewa Matarsa Lema Cike Da Kauna

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.