Har yanzu akwai harsashi a ciki na: Bidiyon labarin fasinjan jirgin Abd-Kad a hannun 'yan bindiga

Har yanzu akwai harsashi a ciki na: Bidiyon labarin fasinjan jirgin Abd-Kad a hannun 'yan bindiga

  • 'Yan bindiga sun sako karin mutane biyar daga cikin mutanen da suka sace a jirgin kasan Abuja zuwa Kaduna
  • Bayan shan iskar 'yanci, daya daga cikin wadanda aka sakan ya yi bayani, inda ya fadi irin halin da suka shiga a hannun 'yan bindigan
  • Hakazalika, ya yi kira ga gwamnati ta taimaka a karbo sauran, wadanda a ciki akwai tsohuwa mai shekaru 90 da yara kanana

Jihar Kaduna - A yau ne biyar daga cikin fasinjojin da ke hannun 'yan bindigan da suka farmaki jirgin Abuja zuwa Kaduna suka kubuta bayan shafe watanni a maboyar 'yan ta'adda.

Daya daga cikinsu ya bayyana irin wahalar da ya sha a hannun 'yan ta'addan, inda ya labarta wani lokaci da aka harbe shi a kasan cibiyarsa amma Allah yasa kwanansa na gaba.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: 'Yan bindiga sun sako karin mutum 5 daga fasinjojin jirgin kasa Abj-Kad da suka sace

A wani bidiyo da Legit.ng Hausa ta gani a shafin Facebook na Ibrahim Sheme, mutanen da suka tsira sun ba da tarihin zamansu a sansanin 'yan bindiga.

Wani ya ba da labarin yadda ya rayu a hannun 'yan bindiga
Fasinjan jirgin Abj-Kad ya ba da labarin yadda 'yan bindiga suka harbe shi, likitansu ya yi masa jinya | Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC

Da yake bayani, mutumin da bai bayyana sunansa ba a bidiyon ya ce:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Alhamdulillahi na kasance daya daya cikin fasinjojin jirgin kasa daga Abuja za mu zo Kaduna, sai kuma iftila'i ya faru da mu.
"Muna hannunsu dai har zuwa kwana 85. Rana irin ta yau, ranar Talata Ina zaune na gama sallar walaha, ina jan carbi ina karanta sunan Allah, Al-Latif sai na ji kara, sai muka ce wannan karan bindiga ne, sai na ce Innalillahi ina ji ma kamar ya same ni.
"Sai na duba sai naga jini ne yake shigowa gajeren wando na. Ina dagawa sai 'yan uwana da muke tare suka ce an harbe ni. Dokta da muke tare dashi sai yace in kwanta."

Kara karanta wannan

An Sha Fama: Bidiyon Yadda Wani Ango Ya Yi Sujjada Tare Da Fashewa Da Kuka A Wajen Daurin Aurensa

Bayan daukar matakan gaggawa na duba lafiyarsa da abokan zamansa da aka kama tare suka yi, daga baya 'yan bindigan sun turo wani likitansu, wanda ya yi ruwa ya yi tsaki wajen gano inda harsashin yake a cikinsa.

A cewarsa:

"Sun turo doktansu ya duba ni, ya sanya yatsarsa a cikin cikina yana laluba inda harsashin yake, amma bai gani ba. Daga baya ya sanya almakashi yana dubawa, ina kara, ina Innalillahi, daga baya dai aka daure min ciwon."

Hakazalika, ya shaida cewa, ya zuwa yanzu dai ba a cire harsashin a jikinsa ba. Kana ya ce yana fatan zuwa asibiti domin duba yadda za a cire harsashin.

Kalli cikakken bidiyon:

Akwai yara kanana da tsohuwa mai shekaru 90 a hannun 'yan bindiga

Da yake karin haske game da wadanda ke hannun 'yan bindigan, ya ce har yanzu akwai saura da dama, daga ciki akwai kananan yara da kuma tsohuwa mai kusan shekaru 90.

Kara karanta wannan

Yadda Malamar Jami’a Ta Koma Tallan Dankali Saboda Yajin Aikin ASUU

Hakazalika, ya yi kira ga gwamnatin tarayya da ta kara kokari wajen ganin an samu mafita an ceto bayin Allah da ke hannun 'yan ta'addan.

'Yan bindiga sun sako karin mutum 5 daga fasinjojin jirgin kasan Abj-Kad

A wani labarin, yanzu muke samun rahoton da ke cewa an sake sakin wasu fasinjoji biyar da aka yi garkuwa da su a harin jirgin kasan Abuja zuwa Kaduna.

Ya zuwa yanzu, an sako akalla mutane 37, wanda kuma har yanzu akwai sauran 35 da ke tsare a hannun 'yan bindiga, kamar yadda Tribune Online ta ruwaito.

Daga cikin fasinjojin da aka saki akwai Farfesa Mustapha Umar Imam, likita a asibitin koyarwa na Jami’ar Usman Dan Fodio (UDUS), Sokoto.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.