Sheikh Bello Yabo ya yi addu'ar Allah yasa a sace Buhari, El-Rufai da Garba Shehu

Sheikh Bello Yabo ya yi addu'ar Allah yasa a sace Buhari, El-Rufai da Garba Shehu

  • Fitaccen malamin addinin Islama ya caccaki gwamnatin Buhari da mukarraban shugaban kasa
  • Bello Yabo ya koka da yadda 'yan Najeriya ke ciki saboda gazawar gwamnati wajen magance matsalar tsaro
  • A makon da ya gabata ne aka ga wani bidiyon dake nuna lokacin da 'yan bindiga ke barazanar sace shugaban kasa Buhari

Najeriya - Shahararren malamin addinin musuluncin nan na Sokoto, Bello Yabo, yayi addu'ar Allah ya hada shugaban kasa Muhammadu Buhari, gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai da mai magana da yawun shugaban kasa, Garba Shehu da 'yan ta'adda.

Addu'ar Bello Yabo na zuwa ne kwanaki kadan bayan fitowar wani bidiyo da ya nuna lokacin da 'yan bindiga ke zabgawa wasu da suka sace bulali tare da yin barazanar sace Buhari da El-Rufai.

Bello Yabo ya roki Allah yasa a sace su Buhari
Sheikh Bello Yabo ya yi addu'ar Allah yasa a sace Buhari, El-Rufai da Garba Shehu | Hoto: dailynigerian.com
Asali: UGC

Garba Shehu ya bayyana martaninsa da ganin bidiyon lakadar fasinjojin jirgin kasan Abuja-Kaduna, inda ya ce ba komai bane face yada farfaganda.

Kara karanta wannan

Babbar matsala sabuwa ta kunno, Wasu Sanatocin APC sun goyi bayan tsige shugaba Buhari

A kalamansa:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Aikin 'yan ta'adda ta hanyar amfani da farfaganda da kuma tada hankali wajen tilastawa gwamnatoci karba ko mika wuya ga bukatun siyasa ba sabon abu bane a duniya."

Martanin Bello Yabo

A nasa martanin ga kalaman Garba Shehu, malamin ya caccaki mai magana da yawun shugaban kasar saboda bayyana bidiyon a matsayin shiri ko kuma farfaganda..

Ya zargi Garba Shehu da cewa bai damu da halin da masu garkuwa da mutane suka sanya mutane ciki ba, ya kuma yi addu’a ga Shehu ya fada hannun masu garkuwa da mutanen, kamar yadda Daily Nigerian ta ruwaito.

Wakilin Leigit.ng Hausa ya bibiyi wani bidiyo da ya yadu a kafar sada zumunta, inda Bello Yabo ke cewa:

"Muna yi musu addu'a masu kamen nan, ya Allah ya baku sa'a ya ku masu kamen nan, ku matsa za mu taimaka muku da addu'a Allah ya baku sa'a ku kamo shi. Wadannan da kuka ce za ku kama ALlah ya baku sa'a ku kamo su. Amma ku sako wadancan da ke hannunku.

Kara karanta wannan

Takarar Yan Addinin Daya Makirci Ne Na Mayar Da Krista Komabaya - Sabon Shugaban CAN

"Idan da irinsu kuke kamawa mu wallahi albarka ma za mu sa muku don sun zama mana bala'i. Meye amfaninsu?"

Hakazalika, malamin ya kuma caccaki yadda gwamnatin Buhari ke tafiyar da lamurran rashin tsaro, a cikin wani bidiyon na daban.

Gani ya kori ji:

Harin Bwari: Sojojin Najeriya sun kashe 'yan ta'adda 30 da suka kai kan sojoji fadar Buhari

A wani labarin, rundunar sojin Najeriya ta tabbatar da ragargazar wasu 'yan ta'adda 30 da ake zargin sun kai hari kan sojojin fadar shugaban kasa a makon nan.

Rahotanni a baya sun bayyana cewa, an kai hari kan sojojin Najeriya a Abuja, inda aka hallaka jami'ai uku tare da jikkata wasu.

Daraktan yada labarai na tsaro, Bernard Onyeuko ya bayyana aikin da jami'an suka yi a wani taron manema labarai na mako bibbiyu kan ayyukan tsaro a ranar Alhamis a Abuja, rahoton Daily Nigerian.

Kara karanta wannan

Fadar Shugaban kasa tayi Martani Mai Zafi ga Sanatocin da ke Yunkurin tsige Buhari

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.