Takarar Musulmi da Musulmi Dabarace Kawai Na Mayar Da Kirista Koma Bayan Musulmi - CAN

Takarar Musulmi da Musulmi Dabarace Kawai Na Mayar Da Kirista Koma Bayan Musulmi - CAN

  • Sabon Shugaban kungiyar kiristocin Najeriya, Archbishop Daneil Okoh ya ce Kristoci na ganin ana kitsa musu markircin mayar dasu koma baya a Najeriya
  • Archbishop Daneil Okoh ya ce mafi akasarin yan siyasan Najeriya ba sa la'akari da bambamcin ra'ayi wajen yanke shawarwari
  • Okoh, ya bukaci Buhari da ya kawo karshen zubar da jini, garkuwa da mutane da rashin tsaro a kasar baki daya

Abuja - Sabon shugaban kungiyar kiristoci ta Najeriya, Archbishop Daniel Okoh, ya ce da yawa daga cikin mabiya addinin kirista suna tsoron cewa ana kitsa makirci da gangan dan mayar da su ‘yan kasa na biyu a Najeriya.

Ya ce fargabar ta samo asali ne daga abubuwan da ke faruwa a harkokin siyasar kasar, wato tikitin tsayar da yan addini daya takara daga cikin daya daga manyan jam'iyyun siyasa a Najeriya duk da jan kune da kungiyar CAN ta yi kada ayi haka.

Kara karanta wannan

Wasu Jihohi 16 Za Su Iya Fusakantar Yunwa da Karancin Abinci inji ‘Yan Majalisa

okohn
Takarar Musulmi da Musulmi Dabarace Kawai Na Mayar Da Krista Koma Bayan Musulmi - CAN Legit.NG
Asali: Depositphotos

Bishof Okoh ya ce:

“Muna lokacin da dukkanin mu mabiya addinin Kirista mun yi imanin cewa wasu shugabannin siyasa ba sa la’akari da bambancin ra’ayi a lokacin da suke yanke wasu shawarwari.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Ya godewa shugaban kasa Muhammadu Buhari bisa kokarin sa da yake yi na yaki da ta’addanci da ‘yan fashi.

Okoh, ya bukaci Buhari da ya kawo karshen zubar da jini, garkuwa da mutane da rashin tsaro a kasar baki daya.

Karin Naira Biliyan 900 Domin Dakile Matsalar Tsaro Yayi Kadan – Lawan

A wani labari kuma, Shugaban Majalisar Dattijai Sanata Ahmad Lawan ya ce Naira biliyan 900 da aka ware don yaki da rashin tsaro a kasar yayi kadan.

Rahoton Daily Trust Lawan, ya bayyana haka ne yayin da yake jawabi ga ‘yan majalisa gabanin dage zaman majalisar dattijai domin hutun shekara, inda ya koka kan yadda ‘yan ta’adda ke kashe-kashe da nakasa ‘yan Najeriya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel