Igiyar leko ta hallaka uwa da 'ya'yan ta hudu a Maiduguri
- Tashin wata wutar gobara daga maganin sauro da wata mata ta kunna ya hallaka ta da 'ya'yan ta hudu
- Wannan hatsari ya faru ne da misalin 12:15 na dare a unguwar Shuwari ta kudu dake garin Maiduguri
- Uwar ta mutu ne yayin da ta shiga cikin wutar domin ceto yaron ta mai shekaru hudu
Tashin wutar gobara daga maganin sauro da wata mata ta kunna ta yi sanadiyar mutuwar matar da 'ya'yan ta hudu.
Wannan hatsari ya faru ne ranar Alhamis da misalin karfe 12:15 na dare a unguwar Shuwari ta kudu dake cikin garin Maiduguri.
Rahotanni sun bayyana cewar uwar yaran Yana ta rasa ranta ne yayin da take kokarin tserar da karamin yaron ta mai shekaru hudu a duniya.
Lamarin ya faru ne yayin da mijin Yana, Adam Bulama, ya yi tafiya zuwa Monguno.
Wani makwabcin gidan Yana, Bana Muhammad, ya shaidawa jaridar Daily Trust cewar, matar ta farka da tsakar dare tana ihun neman taimakon jama'a bayan wuta ta fara cin gidan.
KARANTA WANNAN: Kada ku cakuda siyasa da harkar tsaro - Gwamna Shettima
"Ta fito waje tana ihu, ta na neman a taimaka domin yaran ta na ciki kuma ga gidan na ci da wuta ganga-ganga. Haka ta koma cikin gidan da gudu domin dauko karamin yaron ta mai shekaru hudu amma hayaki da zafin wuta bai bari ta cinma burinta ba," a cewar Bana.
Mai Machina Abubakar, amini ga mijin Yana, ya tabbatar da faruwar lamarin ga Daily Trust tare da cewar tuni aka binne mamatan tun kafin dawowar Bulama.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng