An Ankarar da Jami’an Tsaro Kan Shirin ‘Yan Ta’adda na Kai Hare-Hare a Legas

An Ankarar da Jami’an Tsaro Kan Shirin ‘Yan Ta’adda na Kai Hare-Hare a Legas

  • Rundunar ‘Yan Sandan Najeriya tace ta san da yiwuwar ‘Yan ta’adda su aukawa jihar Legas
  • Kwamishinan ‘Yan Sandan jihar Legas, Abiodun Alabi ya bayyana cewa a shirye dakarunsa suke
  • CP Abiodun Alabi ya yi kira ga mutane su sa-ido, ya kuma bayyana irin kokarin da jami’ai ke yi

Lagos - Mun samu labari cewa rundunar ‘yan sandan Najeriya na reshen jihar Legas suna zaune a cikin shiri bisa zargin hari da ‘yan ta’adda suke shirin kai wa.

Daily Trust ta rahoto cewa Mai magana da yawun bakin rundunar ‘yan sandan reshen jihar, Benjamin Hundeyin, ya fitar da jawabi ya tabbatar da wannan.

A jawabin da SP Benjamin Hundeyin ya fitar a ranar Lahadi, 31 ga watan Yuli 2022, ya nuna suna sane da yiwuwar fuskantar wasu hare-haren ta’addanci a jihar.

Kara karanta wannan

‘Yan Majalisan APC da-dama na goyon bayan mu Tunbuke Buhari inji Sanatan PDP

Kwamishinan ‘yan sanda ya bayyana cewa dakarun jihar Legas sun yi tanadi domin maganin duk wani ko wasu da za su iya kawowa al’umma tashin hankali.

Kakakin ‘yan sandan yake cewa babu mamaki ‘yan ta’addan da suka addabi kasar nan suna harin Legas.

Jawabin Benjamin Hundeyin

“A daidai wannan gaba, Kwamishinan ‘yan sanda na reshen jihar Legas, CP Abiodun Alabi ya ankarar da dakarun SIB su tsaya da shiri.”

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

'Yan Sanda
Wasu Jami'an 'Yan Sanda Hoto: @ngpolice
Asali: Facebook
“Sauran wadanda aka ankarar sun hada da duka shugabannin sassa, jami’an DPO da sauran jagorori domin tabbatar an dakile duk wani hari.”
“Rundunar tana aiki tare da sauran jami’an tsaro domin tabbatar da cewa babu wani ko wadanda suka yi nasarar tada zaune tsaye a Legas."

Rahoton ya nuna Hundeyin ya bayyana cewa an tare iyakoki domin binciken wadanda suke shigowa domin ganin an dakile shigowar duk wasu ‘yan ta’adda.

Kara karanta wannan

Tashin hankali yayin da 'yan bindiga suka farmaki motar kudi, suka hallaka ma'aikacin banki

Har ila yau, jawabin ya yi kira ga mutane su cigaba da gudanar da ayyukansu ba tare da jin tsoro ba.

Hukumar dillacin labarai na kasa, NAN ta rahoto CP Alabi yana kira ga mutanen Legas su sanar da hukuma da zarar sun ga wani motsi da ba su yarda da shi ba.

An sace 'yan wasan kwaikwayo

A makon jiya aka ji kakakin AGN, Monalisa Chinda, tace Kungiyar Nollywood ta girgiza da labarin sace Cynthia Okereke da Clemson Cornell wajen shirya fim.

An ji labari kudin da ake nema kafin a fito da wadannan ‘yan wasan kwaikwayo ya kai N70m idan aka yi la’akari da farashin Dalar Amurka a hannun ‘Yan canji a yau.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng