Hotuna da bidiyo: Dankareriyar daham din da Fatima Shettima ta saka wurin wushe-wushe ya dauka hankali
- A ranar Juma'a ne aka yi shagalin wushe-wushe na auren Fatima Kashim Shettima da kyakyawan angonta Sadiq Bunu
- Babban abin daukar hankali a shigar amaryar shine dankareriyar sarkar daham din da tayi ado da ita tare da awarwaronta
- An ga sarkar ta zauna dirshan a wuyan amarya Fatima inda ta gangaro har zuwa kirjinta cike da birgewa da daukar hankali
A yau ranar Asabar, 30 ga watan Yulin 2022 ne za a daura auren Fatima Kashim Shettima da masoyinta Sadiq Bunu.
Tuni shagulgula suka yi nisa inda aka yi liyafar cin abincin dare a Abuja a makon da ya gabata, aka yi saka lalle sannan a jiya Juma'a aka yi wushe-wushe, liyafa ce da 'yan uwa da abokan arziki amma ta al'adar Kanuri.
Babban abunda ya dauka hankalin wadanda suka ga bidiyoyi da hotunan amarya Fatima shine dankareriyar sarkar gwal dake wuyan amarya.
A bidiyoyin da hotunan, sarkar ta yi zaman dirshan a wuyanta inda ta sauko har zuwa kirjinta yayin da ta saka awarwaro suma masu matukar birgewa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Amaryar ta fito sak Kanuri yayin da ake ta bulbula turaen kamshi a wurin da ta kammala shirin fita wajen liyafar.
Hotunan fitattun 'yan siyasar Najeriya da hamshakan da suka halarci auren diyar Kashim Shettima
A wani labari na daban, a ranar Juma'a, 22 ga watan Yulin 2022 aka yi liyafa cin abincin dare domin karrama Fatima, diyar Kashim Shettima, 'dan takarar mataimakin shugaban kasan jam'iyyar APC da angonta, Sadiq Ibrahim Bunu a Abuja.
Shagalin auren ya samu halartar manyan hamshaka da jiga-jigai a kasa nan kamarsu shugaban majalisar dattawa, Ahmad Lawan, Gwamna Abdullahi Sule na jihar Nasarawa, Gwamna Babagana Zulum na jihar Borno, 'dan takarar shugabancin kasa karkashin jam'iyya APC, Bola Tinubu da sauransu.
Asali: Legit.ng