Cike da tashin hankali, matashi ya sanar da mutuwar budurwar da zai aura nan da sati 2
- Cike da fawwalawa Allah madaukakin Sarki lamurransa, matashi ya sanar da mutuwar budurwarsa da zai aura nan da mako 2
- Safiyanu Abubakar 'dan asalin garin Toro ne a jihar Bauchi kuma ya sanar da mutuwar Rukaiya, wacce zata zama amaryarsa
- Ya kara da bayyana katin daurin auren wanda za a yi a ranar Juma'a, 12 ga watan Augustan 2022, amma amarya ta ce ga garinku
ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit
Rashin masoyi babban ibtila'i ne da kan fadawa 'dan Adam, sau da yawa a kan dade ana jinyar zuciya idan ta rasa abinda take so balle a ce mutuwa ce ta gifta.
Wani matashi mai suna Safiyanu Abubakar ya wallafa katin bikinsa wanda za a yi a ranar 12 ga watan Augutan 2022 da masoyiyarsa Rukaiya Ibrahim Salihu.
Matashin ya bayyana sanarwar mutuwar budurwarsa wacce zasu angwance tare nan da makonni biyu cike da damuwa a shafinsa na Twitter mai suna @SufyToro.
Kamar yadda katin daurin auren ya nuna, masoyan zasu zama mata da miji a ranar Juma'a wurin karfe 1 na rana bayan idar da sallar Juma'a.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
A wallafar matashin yace: "Wacce zan aura ta rasu a daren jiya. Za a daura mana aure a makonni biyu masu zuwa amma a yanzu babu ita. Daga Allah muke, gare shi za mu koma."
Allahu Akbar: Bidiyon mutuwar amarya ana tsaka da liyafar aurenta a jikin angonta
A wani labari na daban, wani bidiyo mai matukar tada hankali ya bayyana a kafar sada zumuntar zamani na Instagram inda aka ga mutuwar amarya ana tsaka da shagalin liyafar aurenta kuma tana hannun mijinta.
A bidiyon da @naija_trending_ suka wallafa a shafnsu na Instagram, an ga amarya da angon zaune a kujera da farko. angon ya rungumo amaryarsa amma sai ta rinjaye shi suka fadi kasa.
Tuni jama'a 'yan biki suka fara tururuwar zuwa inda suke yayin da jikin amarya ya saki ta fadi kasa kuma angon ya bi ta.
Tsokacin Naija Trending din shi ne: "Jama’a mu ji tsoron Allah, Domin ba wanda ya san lokacin mutuwar sa."
Asali: Legit.ng