Satar N109bn na kasa: Kotu ta ba da belin Akanta Janar da aka dakatar

Satar N109bn na kasa: Kotu ta ba da belin Akanta Janar da aka dakatar

  • Kotu a babban birnin tarayya Abuja ta ba da belin akanta janar da ake zargi da sace kudaden Najeriya kana ya azurta kansa
  • A watannin baya ne aka gano wata madakala a ma'aikatar kudi ta Najeriya, inda aka nemi wasu makudan kudade aka rasa
  • An tuhumi akanta janar da satar kudaden da suka kai akalla N109bn tare da wasu mutane da kamfani mai zaman kansa

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Maitama, Abuja - Wata babbar kotun Abuja da ke zamanta a Maitama, a ranar Alhamis, ta ba da belin tsohon Akanta Janar na Tarayya, Ahmed Idris.

Wannan dai na zuwa ne mako guda bayan da kotu ta tasa keyar tsohon AGF din gidan yari, kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.

Aknta ya samu beli bayan sace kudin Najeriya N109bn
Satar N109bn na kasa: Kotu ta ba da belin Akanta Janar da aka dakatar | Hoto: channelstv.com
Asali: UGC

A makon da ya gabata ne kotun ta ba da umarnin a ci gaba da tsare Ahmed Idris da wadanda ake tuhuma tare dashi a gidan yari na Kuje har sai an saurari batun neman belinsu.

Kara karanta wannan

An Yi Latti Ma, Tuntuni Ya Kamata A Tsige Buhari, In Ji Sanata Shehu Sani

Umarnin ci gaba da tsare shi dai ya biyo bayan gurfanar da shi da hukumar yaki da masu yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa ta yi.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Sauran wadanda ake tuhuma da cinye kudin kasar sun hada da Godfrey Olusegun Akindele, Mohammed Kudu Usman da kamfanin Gezawa Commodity Market and Exchange Ltd.

Ana gurfanar da wadanda ake tuhumar ne a kan tuhume-tuhume 14 da suka hada da sata da kuma halasta kudin haram da suka kai N109, 485,572,691.9, rahoton Vanguard.

A hukuncin da ya yanke a yau, alkalin kotun, Mai shari’a Adeyemi Ajayi, ya amince da duk wasu sharuddan belin da hukumar EFCC a baya ta ba tsohon AGF din da wadanda ake karansa tare dasu.

A cewar mai shari'a Ajayi:

“A bisa tsarin da doka ta tanada, wadanda ake tuhumar suna da damar samun beli, ba tare da la’akari da girman tuhumar da ake musu ba.

Kara karanta wannan

Wata sabuwa: Buhari zai sanya takunkumi kan BBC da Aminiya saboda kambama 'yan ta'adda

"Hukumar EFCC ba ta fadi a kowane tsarinta ba, cewa wadanda ake tuhumar sun aikata ba daidai ba yayin da suke kan belin gudanarwa."

Sharuudan belin da aka ba AGF da abokan harkallarsa

Ajayi ya kuma ba da umarnin cewa wadanda ake tuhumar ba za su bar birnin tarayya ba ba tare da izinin kotu ba.

Mai shari’a Ajayi ya yi barazanar soke belin duk wanda ya kasa gurfana gaban kotu a cikinsu a duk sadda aka neme su.

Kotun ta kuma bayyana cewa wadanda ake tuhumar za su sanya hannu kan yarjejeniyar cewa za su bi sharuddan belin da EFCC ta gindaya.

Mai shari’a Ajayi ya kuma ba da da umarnin cewa wadanda ake tuhumar kada su samu damar ganin fasfo dinsu har sai an kammala shari'ar, kana kada a basu damar yin sabo.

Ajayi ya yanke hukuncin ne bisa hujjar cewa har yanzu ba a tabbatar da zargin da ake yi wa wadanda ake tuhumar ba.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu : Kotu Ta Bada belin Dakataccen Akanta-Janar

Yanzu dai an fara gudanar da shari’ar akanta nan take bayan yanke hukuncin ba da belinsa.

EFCC ta gano sabbin N90bn da AGF Ahmed Idris ya wawure, ya tona asirin minista da wasu jiga-jigan gwamnati

A wani labarin, bincike kan makuden kudaden da hukumar yaki da rashawa tare da hana yi wa tattalin arzikin kasa ta'annati, EFCC, game da dakataccen akanta janar na tarayya, Ahmed Idris, ya haura ya kai N170 biliyan, rahoton jaridar The Nation ya bayyana.

Idris, wanda a daren jiya ya ke neman a bada belinsa, ya bayyana sunayen wasu manyan jami'an gwamnati da ke da hannu cikin handamar kudaden kasar da ake tuhumarsa a kai.

Hukumar EFCC ta tuhumi wani babban sakataren gwamnati kan wasu daga cikin kudaden da ake zarginsa da rub da ciki a kai.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.