Mun san za a yi adalci: Mahaifan marigayiya Hanifa sun yi martani bayan hukunta malaminta

Mun san za a yi adalci: Mahaifan marigayiya Hanifa sun yi martani bayan hukunta malaminta

  • Bayan yankewa makashin Hanifa hukuncin kisa ta hanyar rataya, mahaifin yarinyar ya fito ya yi bayani
  • A karshen shekarar da ta gabata ne aka sace wata yarinya mai shekaru biyar a Kano, daga bisani aka samu ta mutu
  • Malaminta ne aka ruwaito ya sace ta, wanda kuma ya amsa cewa ya kashe ta da hannunsa da gubar bera

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Jihar Kano - Bayan kai ruwa rana a kotu, an yankewa Abdulmalik Tanko hukuncin kisa ta hanyar rataya bisa kama shi da laifin sacewa, kashewa gami da wulakanta gawar dalibarsa Hanifa Abubakar.

Jim kadan bayan hukuncin, iyayen marigayiyar sun fito sun yi bayani, inda suka bayyana irin yanayin da suka shiga da jin hukuncin da aka yanke wa makashin diyarsu.

A wani bidiyon da jaridar Aminiya ta yada a kafar sada zumunta ta Twitter, Legit.ng Hausa ta ji irin martanin mahaifin Hanifa da ma na mahaifiyarta.

Kara karanta wannan

Daga Ƙarshe, Kotu Ta Yanke Wa Abdulmalik Tanko Da Hashimu Hukuncin Kisa Bisa Laifin Kashe Hanifa Abubakar

Martanin mahaifin Hanifa Abubakar bayan hukunta Abdulmalik
Mun san za a yi mana adalci: Iyayen marigayiya Hanifa sun yi martani bayan hukunta malaminta | Hoto: dailytrust.com
Asali: Instagram

Da yake magana da manema labarai a harabar kotun, mahaifin Hanifa, Abubakar Abdulsalam ya bayyana cewa:

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

"Ban taba tunanin cewa ba zai mana adalci ba, to tunda Allah yasa an yi adalci babu abin da zamu iya cewa jama'a sai godiya. Addu'o'i na jama'a, da wadanda suka saka mu addu'o'i Allah ya muku albarka. Allah ya mai da kowa gida lafiya. Mun gode, mun gode Alla ya saka wa kowa da alheri."

Ita kuwa mahaifiyar, wakilinmu ya lura da irin halin da take ciki na kunci ganin yadda take zubar da kwalla, kana ta gagara cewa komai sai godewa Allah.

Batun zartar da hukuncin kisa ga makashin Hanifa

Da aka tambaye shi game da kwarin gwiwar da yake dashi kan zartar da hukuncin na kotu, mahaifin Hanifa ya ce, wannan kuma batu ne na kotu, kuma yana hannunsu.

Kara karanta wannan

Bana Wasa Da Jin Dadin Iyalina Ko Kadan Kuma Ina Shirin Rufe Kofa Da ta Hudu, Lakcara mai yara 18

Hakazalika, ya kuma tuna da alkawarin gwamnan jihar Kano na cewa za a tabbatar da zartar da hukuncin da kotu ta yanke.

Ya kuma bayyana cewa, yana kwarin gwiwar gwamna Ganduje ba zai saba alkawarin da ya yi na cewa zai sanya hannu kan zartar da hukuncin na kotu ba.

Yadda lamarin ya faro

A ranar biyu ga watan Disamban 2021 ne aka sace Hanifa Abubakar, yarinya mai shkaru biyar a jihar Kano a hanyar dawowa daga makarantar Islamiyya, inda ta shafe lokaci ana nema ba a gano inda take ba.

Bayan dogon bincike cikin tsanaki na jami'an 'yan sandan Najeriya, an gano cewa, malaminta kuma mai makarantar da take karatu ne ya sace ta domin karbar kudin fansa daga iyayenta, kamar yadda PM News ta ruwaito.

Rahotanni sun ce, tuni dama malamin mai suna Abdulmalik ya karbi wasu kudade daga iyayen yarinyar, duk da cewa ya riga ya kashe ta.

Kara karanta wannan

Tashin hankali a Abuja yayin da aka garkame makarantar sakandare saboda tsoron harin 'yan bindiga

Bayan shiga hannu, an garzaya dashi kotu, wannan kuma ya kai ga hukuncin da aka yanke masa a yau na kisa ta hanyar rataya.

Ga dai abinda yake cewa:

Mazauna Kano: Dalilin da yasa aka kori makashin Hanifa daga makarantar da ya koyar shekaru 3 da suka shige

A wani labarin, Daily Trust ta ce karin bayanai sun bayyana kan Abdulmalik Tanko, shugaban makarantar Noble Kids Academy, Kwanar Dakata da ke karamar hukumar Nasarawa ta jihar Kano.

Labarin Tanko dai ya karade ko'ina a fadin kasar bayan an kama shi kan laifin garkuwa da kuma kashe Hanifa Abubakar, wata daliba mai shekaru 5 a makarantarsa.

Wani mazaunin karamar hukumar Nasarawa ya bayyana cewa an sallami Tanko ne daga wata makarantar kudi, Ete Inoh International School, a Tudun Wada, inda ya karantar sannan ya yi aiki a matsayin shugaba bisa zargin karkatar da kudade, rahoton Daily Trust.

Kara karanta wannan

Tashin hankali: 'Yan fashi da makami sun dura wani coci, sun yiwa fasto da mabiyansa tas

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.