Gwamnatin Buhari za ta sanya takunkumi kan BBC da Aminiya saboda kambama 'yan ta'adda

Gwamnatin Buhari za ta sanya takunkumi kan BBC da Aminiya saboda kambama 'yan ta'adda

  • Gwamnatin Buhari na duba yiwuwar daukar mataki kan kafafen yada labarai da ke kambama 'yan ta'adda a Najeriya
  • Aminiya da BBC na daga cikin gidajen yada labarai da ke ganawa da 'yan ta'adda tare da fitar da rahoto a kansu
  • A karshen makon jiya ne 'yan ta'adda suka yi barazanar sace shugaban kasa Muhammadu Buhari da gwamna El-Rufai

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

FCT, Abuja - Gwamnatin tarayya ta ce za ta sanya takunkumi ga gidajen rediyon Birtaniya (BBC) da jaridar Daily Trust, mai wallafa sashen Hausa na Aminiya kan shirin da suka tattara kan ta’addanci da barnar ‘yan bindiga a Najeriya a kwanan nan.

Lai Mohammad, ministan yada labarai da al'adu ne ya bayyana hakan a Abuja ranar Alhamis, The Cable ta ruwaito.

A kwanan nan ne wasu fafa-fayan bidiyo suka yadu a kafafen sada zumunta, inda ake nuna wakilan BBC da na Aminiya suna hira da 'yan ta'adda a cikin dazukan da suke fake.

Kara karanta wannan

Yanzun nan: Buhari ya yi martani kan barazanar tsige shi da sanatocin PDP suka yi

FG za ta sanya wa BBC da Daily Trust takunkumi saboda kambama 'yan ta'adda
Babbar magana: Gwamnatin Buhari za ta saka wa BBC da Daily Trust takunkumi saboda kambama 'yan ta'adda | thecable.ng
Asali: UGC

A cewar Lai Mohammed:

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

"Ina mai tabbatar muku, ba za su tsira da wannan aiki na kambama ta'addanci da 'yan bindiga ba a Najeriya.
"Lokacin da wasu kafafe masu daraja irin su BBC ke ba wa 'yan ta'adda kafafensu, suna nuna fuskokinsu kamar su taurarin Nollywood ne... Ina so in tabbatar musu da cewa ba za su yi tsira ba, za a sanya takunkumin da ya dace a kansu.
“Abin da zan iya cewa shi ne akwai wata hukuma mai kula da harkokin yada labarai ta Najeriya (NBC) kuma suna sane da wadannan abubuwan da suka faru kuma suna duban wane bangare na ka’idojin yada labarai ne BBC da Daily Trust suka karya."

A cikin wani shirin bidiyo mai tsawon mintuna 50 mai suna ‘Bandit Warlords of Zamfara’, da BBC Africa Eye ta wallafa ya yi binciken rayuwar 'yan bindiga a cikin dazuka.

Kara karanta wannan

An kai wa 'Dan Majalisar Daura, 'Danuwan Shugaba Buhari Hari Har Gida a Katsina

Hakazalila, bidiyon ya nuna yadda karuwar satar mutane ke ta'azzara, da kuma yadda rashin tsaro a Zamfara ya faro ta rikicin kabilanci tsakanin Hausawa da Fulani.

A watan Maris din bana, Daily Trust/Aminiya, ya buga rahoto na musamman da shirin da ya bankado manyan batutuwan da suka shafi ‘yan bindiga a Najeriya. An yi hira da 'yan ta'addan da suka addabi Arewa irinsu Bello Turji da dai sauransu.

Bello Kachalla, wanda aka fi sani da Turji, sanannen kasurgumin 'yan bindiga ne da ke addabar Arewacin Najeriya, musamman jihohin Zamfara, Sokoto da Neja.

Gwamnatin Buhari ta yi martani kan barazanar da Sanatocin PDP suka yi na tsige Buhari saboda rashin tsaro

A wani labarin, gwamnatin tarayya ta mayar da martani kan barazanar da Sanatocin jam’iyyar PDP suka yi na tsige shugaban kasa Muhammadu Buhari, The Cable ta ruwaito.

A ranar Laraba ne ‘yan majalisar suka baiwa shugaban kasar wa’adin makwanni shida domin ya magance matsalar rashin tsaro ko kuma ya fuskanci batun tsige shi.

Kara karanta wannan

Bidiyon Rahama Sadau Tana Zuba Yaren Indiyanci, Za Ta Fito A Shirin Bollywood

Da yake magana bayan taron majalisar zartarwa ta tarayya (FEC), Lai Mohammed, ministan yada labarai, ya ce gwamnatin tarayya tana aiki ba dare ba rana don ganin ta magance matsalolin tsaro.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.