Yanzu-Yanzu: Tawagar marasa rinjaye ta Majalisar Dokoki sun shiga ganawar sirri
- 'Yan majalisun PDP a majalisar kasa sun amince da kudurin majalisar dattawa na ba shugaba Buhari wa'adin kawo karshen rashin tsaro
- A jiya ne sanatocin PDP suka dage dole shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kawo karshen ta'addanci cikin makwanni shida
- Wannan kira ya haifar da hargitsi tsakanin 'yan majalisun, lamarin da ya ba 'yan Najeriya da dama mamaki
FCT, Abuja - ‘Yan majalisa karkashin kungiyar marasa rinjaye a majalisar dokokin kasar nan sun yi shigar ganawar bayan fage a yau Alhamis 28 ga watan Yuli
Gidan talabijin na Channels ta ruwaito cewa, ta yiwu ganawar ba za ta rasa nasaba da shirin tsige shugaba Muhammadu Buhari ba, kamar yadda aka tado da batun a baya.
Taron dai ya zama dole ne don tattauna yiwuwar zama a bangare guda kan bukatar ‘yan majalisar dattawa da na marasa rinjaye a kan abin da ya dumfaro a majalisar jiya Laraba kan barazanar tsige shugaban kasa.
Shugaban marasa rinjaye na majalisar wakilai, Ndudi Elumelu, ya yiwa manema labarai karin haske bayan kammala taron na sirri kan batun da aka tattauna.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya shaida cewa ‘yan majalisar marasa rinjaye za su yi gama kai da majalisar dattawa a wa’adin makwanni 6 ga shugaban kasa kuma za’a tattara sa hannun 'yan majalisun don tsige Buhari idan bai magance matsalar tsaro ba.
Ya kuma ja hankali kan halin da al'ummar kasar ke ciki, daga ciki har da matsalar musayar kudi da faduwar darajar Naira da matsalar jiragen sama.
Punch ta ruwaito cewa, 'yan majalisun na PDP sun amince da kudurin sanataocin PDP na tsige Buhari idan ya gaza kawo karshen rashin tsaro a cikin makwanni shida.
Lalacewar Naira: Majalisar dattawa ta gayyaci gwamnan CBN yayin da dala ta kai N700
A wani labarin, majalisar dattawa ta gayyaci gwamnan babban bankin Najeriya (CBN), Godwin Emefiele, kan faduwar darajar Naira.
Hakan ya biyo bayan kudirin da Sanata Olubunmi Adetunmbi (APC, Ekiti ta Arewa) ya gabatar, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.
A halin yanzu dai darajar Naira bai wuce tsakanin N690 zuwa N700 ba kan kowacce dala a kasuwanni.
Asali: Legit.ng