Yan bindiga sun kashe Mutane 20 a Yankunan Jihar Zamfara

Yan bindiga sun kashe Mutane 20 a Yankunan Jihar Zamfara

  • An gano gawarwaki 20 kusa da wani rafi da yan bindiga suka kai hari a kauyukan Yan-Kukoki da Danbanda a karamar hukumar Gummi
  • Mutanen kauyukan Yan-Kukoki da Danbanda sun buya a daji a lokacin da yan bindiga suka kawo musu hari
  • Daya daga cikin shugabannin kauyen Zamfara ya ce mako daya kafin a kawo musu harin sun ga alamar kai da komowar ’yan bindigar a yankin

Jihar Zamfara - Kimanin gawarwaki 20 aka gano a kusa da wani rafi, kwana guda bayan wasu da ake kyautata zaton ‘yan bindiga ne suka kai hari a kauyukan Yan-Kukoki da Danbanda a karamar hukumar Gummi a jihar Zamfara. Rahoton TheCable

Daya daga cikin mazauna yankin da suka tsere daga harin ya shaidawa jaridar TheCable cewa ‘yan bindigar sun zo ne da safiyar Laraba kuma aniyarsu ta satar shanu ne.

Kara karanta wannan

Tashin hankali yayin da 'yan bindiga suka farmaki motar kudi, suka hallaka ma'aikacin banki

Amma an ce mutanen kauyen sun buya a daji ne lokacin da ‘yan fashin suka fara harbe-harbe.

gunmen
Yan bindiga sun kashe Mutane 20 a Yankunan Jihar Zamfara Legit.NG
Asali: UGC

Wasu sun gudu, wasu kuma sun fada cikin rafi, yayin da aka harbe wasu. A yanzu an kirga gawarwaki guda 20.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Mazauna yankin da suma suka zanta da TheCable sun ce sun yi zargin ‘yan bindigar suna ta sinitiri a yankin kusan mako guda kafin a kawo musu harin.

Sai dai da aka tuntubi Kakakin ’Yan Sandan Jihar, SP Muhammed Shehu, ya karyata labarin kai hari, inda ya ce yanzu haka ma yankin na nan zaune lafiya.

Borno: Yan Boko Haram Sun Kai Wa Tawagar Shugaban Ƙaramar Hukuma Hari, Sun Kashe Ɗan Sanda

A wani labari kuma, Ɗan sanda ya riga mu gidan gaskiya a yayin da wasu da ake zargin yan Boko Haram ne suka kai wa tawagar motocin shugaban karamar hukumar Nganzai a Jihar Borno, Hon Asheikh Mamman Gadai, hari a ranar Laraba.

Kara karanta wannan

Tashin hankali: Wani rahoton sirri ya fallasa, 'yan ta'adda sun tara makamai za su afkawa jihar Buhari

Lamarin ya faru ne a hanyar Gajiram da Gajiganna lokacin da Asheikh da tawagarsa ke hanyarsu ta zuwa wani aiki, rahoton Daily Trust.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Tofa avatar

Ibrahim Tofa