Siyasa: Ana neman dan a mutun Peter Obi da ya yi barazanar kashe jama'ar Atiku da Tinubu

Siyasa: Ana neman dan a mutun Peter Obi da ya yi barazanar kashe jama'ar Atiku da Tinubu

  • Rahotanni sun bayyana cewa jami’an tsaro sun fara farautar wani matashin da har yanzu ba’a tantance ko wanene ba, wanda yayi barazanar kashe magoya bayan Atiku da Tinubu a yankin Kudu maso Gabas
  • Matashin dai, a wani faifan bidiyo da aka yada a kafar sada zumunta ya gargadi duk wanda ba zai zabi Peter Obi ba da ya nisanci rumfunan zabe a yankin
  • Wata majiyar tsaro da ta tabbatar da fara farautarsa, ta ce ana zargin matashin dan kungiyar IPOB ne da ke ta'addanci a yankunan Kudu maso Gabas

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Najeriya - Jami’an tsaro sun fara farautar wani mutum da har yanzu ba a gano waye shi ba ya yi barazanar kashe duk wanda ya zabi Atiku Abubakar na PDP da Asiwaju Bola Tinubu na APC a zaben shugaban kasa na 2023 a yankin Kudu maso Gabas.

Kara karanta wannan

El-Rufai: Buhari Bai Ma San Yan Ta'adda Sun Yi Barazanar Sace Shi Ba, Sai Da Na Sanar Da Shi

A wani faifan bidiyo da aka yi ta yadawa a shafukan sada zumunta, matashin, wanda aka gani yana nuna wani abu kamar wata ‘yar bindigar kirar gida, ya gargadi magoya bayan ‘yan takarar shugaban kasa na APC da PDP da kada su fito kada kuri’a idan ba za su zabi Peter Obi ba.

Matashi ya yi barazanar harbe duk wanda ya zabi Tinubu ko Atiku a 2023
Siyasa: Ana neman dan a mutun Peter Obi da ya yi barazanar kashe jama'ar Atiku da Tinubu | Hoto: Atiku Abubakar, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Asali: UGC

Ya gwada bindigar domin ya tabbatar da cewa ba ta wasa ba ce, kana ya gargadi wadanda ba za su zabi Peter Obi ba, dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Labour kuma tsohon gwamnan jihar Anambra, da su nisanci rumfunan zabe.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Nan ba da jimawa ba za a kama shi, in ji majiyar tsaro

Sai dai kuma, PR Nigeria, ta nakalto majiyar tsaro da ba a bayyana sunanta ba, ta ce nan ba da jimawa ba za a kama matashin saboda mummunar barazanar da ya yi.

Kara karanta wannan

Yanzun nan: Buhari ya yi martani kan barazanar tsige shi da sanatocin PDP suka yi

A cewar majiyar:

“Saurayin, wanda ake zargin dan kungiyar IPOB ne ya yi barazanar ‘kisa’ a wani faifan bidiyo mai tsawon dakika 30 wanda aka yada a kafafen sada zumunta daban-daban.
“Abin takaici ne kuma abin damuwa ne ganin yadda dan ta'addan ya sha alwashin cewa zai fito 2023, zai harbe mutane da kashe su a rumfunan zabe, idan suka yi yunkurin zaben Atiku ko Tinubu.”

Gwamnatin Buhari ta yi martani kan barazanar da Sanatocin PDP suka yi na tsige Buhari saboda rashin tsaro

A wani labarin, gwamnatin tarayya ta mayar da martani kan barazanar da Sanatocin jam’iyyar PDP suka yi na tsige shugaban kasa Muhammadu Buhari, The Cable ta ruwaito.

A ranar Laraba ne ‘yan majalisar suka baiwa shugaban kasar wa’adin makwanni shida domin ya magance matsalar rashin tsaro ko kuma ya fuskanci batun tsige shi.

Da yake magana bayan taron majalisar zartarwa ta tarayya (FEC), Lai Mohammed, ministan yada labarai, ya ce gwamnatin tarayya tana aiki ba dare ba rana don ganin ta magance matsalolin tsaro.

Kara karanta wannan

2023: Kwankwaso Da Peter Obi Duk 'Yan Kallo Ne, Zabe Tsakanin Tinubu Da Atiku Ne, Gwamna Sule

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.