Kano: Ganduje Ya Bada Hutu Don Murnar Sabuwar Shekarar Musulunci ta 1444

Kano: Ganduje Ya Bada Hutu Don Murnar Sabuwar Shekarar Musulunci ta 1444

  • Gwamnatin Jihar Kano ta ayyana ranar Litinin a matsayin ranar hutu domin murnar shiga sabon shekarar musulunci
  • Gwamna Abdullahi Ganduje cikin sanarwar da Kwamishinan Labarai, Mohammad Garba ya fitar ya taya musulmin jiharsa murnar shiga sabuwar shekarar
  • Ganduje ya bukaci mutanen jihar su yi amfani da hutun domin tuba ga Allah su kuma yi wa kasa addu'a Allah ya magance kallubalen tsaro da ake fama da shi

Jihar Kano - Gwamnatin Jihar Kano ta ayyana ranar Litinin a matsayin ranar hutu, domin murnar sabuwar shekarar musulunci ta 1444 A.H.

Hakan na cikin sanarwar da kwamishin labarai, Mohammad Garba ya fitar a Kano kamar yadda Daily Nigerian ta rahoto.

Gwamna Abdullahi Ganduje.
Kano: Ganduje Ya Bada Hutu Don Murnar Sabuwar Shekarar Musulunci. Hoto: @daily_nigerian.
Asali: Twitter

"Gwamna Abdullahi Ganduje, yana taya musulmi a jihar murnar sabuwar shekarar ya kuma yi kira ga mutane su yi wa kansu hisabi.

Kara karanta wannan

Rashin Tsaro: Gumi Ya Ragargaji Gwamnatin Najeriya Kan Barazanar Hukunta BBC Da Aminiya

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

"Ya kuma yi kira gare su suyi amfani da hutun domin neman gafarar Allah, kuma su yi addu'a Allah ya ceci kasar daga kallubalen tsaro da ta ke fama d ashi," in ji shi.

Ya bawa mazauna jihar tabbacin cewa gwamnatinsa za ta cigaba da aiki domin inganta rayuwarsu ta hanyar aiwatar da ayyuka na cigaban mutane.

Ganduje ya kuma yi kira ga wadanda har yanzu ba su karbi katinsu na zabe ba, su yi hakan, domin samun damar kada kuri'arsu a babban zabe da ke tafe.

Muharram ce watan farko na kalandar musulunci, kuma ita ce wata mafi girma bayan watan Ramadan.

Sarkin Musulmi ya bada umurnin a fara neman jinjirin watan Muharram

Sarkin Musulmi, Sa'ad Abubakar III, ya umurci musulmi su fara neman jinjirin watan Muharram daga yau Alhamis, wanda ya yi dai-dai da 29 ga watan Dhul-Hijjah shekarar 1443 bayan hijira.

Kara karanta wannan

Cike da tashin hankali, matashi ya sanar da mutuwar budurwar da zai aura nan da sati 2

Dukkan kwanakin wata a kalandar musulunci na 2022 sun dogara ne da ganin wata.

Jigon Jam'iyyar APC a Kano, Injiniya Bashir, Ya Fita Daga Jam'iyyar

A wani rahoton, tsohon mai neman takarar gwamnan kuma jigo a jam'iyyar APC, Bashir I. Bashir ya fice daga jam'iyyar mai mulki, rahoton Daily Nigerian.

A cikin wasika da ya aike wa shugaban jam'iyyar na APC a gundumar Alawa, karamar hukumar Gaya a Jihar Kano, Mr Bashir ya gode wa shugaban jam'iyyar bisa goyon baya da hadin kai da ya bashi.

Ya shaidawa yan jarida cewa nan da kwanaki kadan sai sanar da jam'iyyar da zai koma.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164