Tashin hankali: 'Yan bindiga sun kai hari kan motar kudi, sun hallaka ma'aikacin banki

Tashin hankali: 'Yan bindiga sun kai hari kan motar kudi, sun hallaka ma'aikacin banki

  • Rundunar 'yan sandan jihar Abia ta bayyana yadda 'yan bindiga suka yi musayar wuta da 'yan sanda a jihar
  • An harbe dan sanda daya, an kuma harbi daya daga cikin 'yan bindigan a shirinsu na yin awon gaba da motar banki
  • Ana yawan samun hare-haren kan motocin da ke jigilar kudade tsakanin jihohi ko kananan hukumomi a Najeriya

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Jihar Abia - Rundunar ‘yan sandan jihar Abia ta ce an kashe wani jami’in banki, biyo bayan wani hari da aka kai kan wata motar kudi a jihar, The Cable ta ruwaito.

Geoffrey Ogbonna, kakakin rundunar ‘yan sandan Abia ne ya tabbatar da faruwar lamarin a ranar Laraba 27 ga watan Yulin 2022.

'Yan bindiga sun farmaki motar banki a Abia
Tashin hankali: 'Yan bindiga sun hari motar banki, sun saci kudi, sun hallaka ma'aikata 3 | Hoto: vanguardnhr.com
Asali: Facebook

A cewarsa, ‘yan bindigar sun kai harin ne a ranar Talata a mahadar Ntigha, kusa da Umuahia, babban birnin Abia.

Kara karanta wannan

Tashin hankali: Wani rahoton sirri ya fallasa, 'yan ta'adda sun tara makamai za su afkawa jihar Buhari

Ya ce motar ta dauko kudi ne daga bankin Aba zuwa Umuahia lokacin da ‘yan bindigar suka yi musu kwanton bauna.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Rahoton ya ce, an harbe wani jami’in bankin, kan an harbe daya daga cikin ‘yan bindiga yayin musayar wuta.

Ya kuma bayyana cewa, jami'an 'yan sanda shida ne ke kan rakiya a lokacin da lamarin ya faru.

An lissafa kayayyakin da aka kwato daga hannun maharan a matsayin bindiga kirar AK-47 guda daya, da kuma harsashi a cikin mujallu uku, rahoton Premium Times.

Ogbonna ya ce uku daga cikin jami’an sun samu raunuka na harbin bindiga kuma an kai su asibiti, yayin da aka ajiye marigayin a dakin ajiyar gawa.

Kakakin ‘yan sandan ya kara da cewa an fara gudanar da bincike kan lamarin.

Ya kuma yi kira ga mazauna yankin da ma’aikatan lafiya da su kai rahoton duk wanda aka gani da harbin bindiga ga hukumomin tsaro.

Kara karanta wannan

An samu hargitsi yayin da aka kama wasu 'yan sa kai na bogi a wurin zanga-zangar 'yan kwadago da ASUU

Borno: Sojoji sun sake ceto ‘yan mata 2 na makarantar Chibok da Boko Haram suka sace

A wani labarin, akalla shekaru takwas bayan kai mummunan hari Chibok da kuma sace 'yan mata a wata makarantar sakadaren garin, rundunar soji ta kubutar da wasu daga cikin 'yan matan.

A rahoton da muka samo daga jaridar Leadership, an ce jami'an sun ceto biyu daga cikin 'yan matan sama da 200 da aka yi garkuwa dasu kuma aka yi musu auren dole tun shekarar 2014.

Wani rahoton sirri daga manyan majiyoyin tsaro, sun tabbatar da ceto 'yan matan daga sansanin Gazuwa, wata hedikwatar kungiyar Boko Haram da aka fi sani da Gabchari, Mantari da Mallum Masari, mai tazarar kilomita tara zuwa garin Bama.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.