2023: Cocin Anglican Ta Fada Wa Kiristoci Abin Da Za Su Yi Game Da Tikitin Musulmi Da Musulmi Da APC Ta Yi
- Cocin Anglican ta Najeriya ta soki jam'iyyar APC mai mulki a kasa kan tsayar da musulmi a matsayin dan takarar shugaban kasa da mataimaki a zaben 2023
- Rabaran Dakta Duke Akamisoko, Bishop din Anglican na Abuja ne ya yi wannan sukar yayin hira da manema labarai a ranar Laraba a Abuja
- Akamisoko ya ce cin fuska ne ga kirista ya kuma bukaci kiristocin su nuna wa APC zabinsu tunda jam'iyyar yayin zabe tunda ta nuna abin da ta zaba ita ma
Abuja - Cocin Anglican ta Najeriya, a ranar Laraba, ta yi suka da kakkausan murya ga jam'iyyar APC kan dagewa game da batun tsayar yan takarar shugaban kasa musulmi da musulmi, duk da kokawa da yan kasar suka yi.
Cocin ta ce rashin sanin ya kamata ne jam'iyyar ta fifita nasarar ta kan hadin kai da zaman lafiya a kasar, rahoton The Punch.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Bishop din Anglican na Kubwa, Rabaran Dakta Duke Akamisoko, ne ya sanar da hakan cikin hira da ya yi da manema labarai a Abuja.
Ya bayyana tsayar da tikitin musulmi da musulmi da jam'iyyar ta yi a matsayin abin da cocin ba za ta lumunta ba; ya kara da cewa hakan 'nuna halin ko in kula ne ga yadda kasar ke ciki.'
APC ta yi zabinta, ku ma ku yi naku, Akamisoko ya fada wa Kiristocin Najeriya
"Tikitin musulmi da musulmi a irin wannan lokacin ya nuna ba a damu da sauran addinai ba; koken kiristocin Najeriya ke ciki da halin da kiristocin arewacin Najeriya ke ciki ds.
"Hasali ma, wannan cin mutunci ne karara ka dukkan kiristoci. APC ta yi zabinta; ya rage ga sauran kiristocin Najeriya suma su yi zabinsu," in ji Akamisoko.
Ya cigaba da cewa:
"Ba bu wani sahihin dalili na yin wannan zabin na son kai da hadama da APC ta yi. Rashin sanin ya kamata ne APC ta zabi burinta na siyasa kan daidaito da zaman lafiyar Najeriya.
"Ya kamata jam'iyyar ta dauki darasi saboda rashin amincewar kuma ta yi koyi da Shugaba Muhammadu Buhari yadda ya zabi mataimaki kirista a 2015 a maimakon yin tikitin musulmi da musulmi.
"Tikitin musulmi da musulmi shine babban cin fuska ga Kiristoci, musamman na arewa. Shin APC na cewa babu kirista a Arewa wanda ya cancanci zama mataimaki? APC na cewa babu kirista a arewa wanda zai iya kawo mata nasara? Tabbas, amsar ita ce A'a."
Malamin addinin kiristan ya kuma tofa albarkacin bakinsa kan wasu batutuwa a kasar kamar yajin aikin ASUU, rashin tsaro, yaki da rashawa da babban zaben 2023 da wasu.
Asali: Legit.ng